Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata Akpabio

Majalisa Ta 10: Gwamna Wike Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata Akpabio

  • Gwamnan jihar Rivers ya nuna goyon bayansa ga kuɗirin sanata Godswill Akpabio na zama shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Gwamna Nyesom Wike ya bayyana cewa zai tsaya kai da fata domin ganin Akpabio ya zama shugaban majalisar
  • Wike ya ce yanzu lokacine na mayarwa da Akpabio biki ne saboda goyon bayan da ya ba shi a baya lokacin yana son zama gwamnan Rivers

Abuja - Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, ya ce zai goyi bayan sanata Godswill Akpabio, ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10, rahoton The Nation ya tabbatar.

Wike ya bayyana goyon bayansa ne ga Akpabio, lokacin da sanatan da mambobin Stability Group, wata tawagar zaɓaɓɓun sanatoci masu goyon bayan Akpabio, suka ziyarce shi a ƙarƙashin jagorancin, babban darektanta sanata Ali Ndume.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

Wike ya goyi bayan Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa
Sanata Godswill Akpabio tare da gwamna Nyesom Wike Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Gwamna Wike zai mayar da biki

Jaridar Vanguard tace a wata sanarwa da ofishin yaƙin neman zaɓen sanata Godswill Akpabio, ya fitar a birnin tarayya Abuja, gwamna Wike ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan lokaci ne da zan marawa (Akpabio) baya, saboda ya goya min baya lokacin da na ke son zama gwamnan jihar Rivers."
"Idan har tabbas mu na son ƙasar nan ta ci gaba daga matakin da ta ke ciki a yanzu, ban ga wani aibu ba don jam'iyya mai mulki ta zaɓi wanda ta ke ganin zai iya aiki tare da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10."
"A dangane da tafiyar Akpabio da Barau, mu na cikinta domin tabbatar da cewa sun samu nasara."
"Wannan lokacin mayar masa da biki ne. Zan goyi bayansa har sai ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba. Nan ba da jimawa ba za mu tattauna da tawagata domin cimma matsaya kan muradinsa."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Kulla-Kullar Dawo Da Ahmed Lawan a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10

Ahmad Lawan Ya Nesanta Kansa Da Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa

Rahoto ya zo cewa shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan ya musanta cewa yana cikin, masu takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Sanata Ahmad Lawan ya fito fili ya bayyana cewa ƙarya ce tsagwaronta kawai ake masa ta cewa ya shiga ƴan takara cikin masu neman ɗarewa shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel