Ku Rantse da Allah Ba Ku Saci Dukiyar Talakawa Ba, El-Rufai Ya Kalubalanci Tsofaffin Gwamnonin Kaduna

Ku Rantse da Allah Ba Ku Saci Dukiyar Talakawa Ba, El-Rufai Ya Kalubalanci Tsofaffin Gwamnonin Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana kalubale ga tsoffin gwamnonin jihar a daidai lokacin da ya kusa barin kujerar mulki
  • Malam Nasir El-Rufai ya ce bai taba satar kudin talakawa ba kamar wasu tsoffin gwamnonin jihar ta Kaduna
  • Ya ce idan akwai gwamnan da bai saci kudin talakawa ba, to ya fito ya kalli mutanen jihar ya rantse da Allah

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna mai barin gado, Malam Nasiru El-rufai ya fito balo-balo ya nemi tsoffin gwamnonin jihar da su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su sace dukiyar talakawa a lokacin da suke kan mulki ba.

El-rufai ya yi wannan batu ne a cikin hirarsa ta kafafen yada labarai na Sashen Hausa na Hukumar Yada Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC), Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba Sassauci: Yana Dab Da Sauka Mulki, Gwamna El-Rufai Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

A cewar El-rufai, daya daga cikin tsoffin gwamnonin ya ma gina wani katafaren gida a kan titin Jabi da ke GRA a Kaduna, da kudin sata na talakawan jihar.

Malam Nasiru ya kalubalanci tsoffin gwamnonin Kaduna
Malam Nasiru Ahmad El-Rufai | Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Idan ba tsoro ba gwamnonin da suka shude su fuskanci al’ummar jihar Kaduna su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba sata daga asusun gwamnati ba.”

Ban taba satar kudin ‘yan Kaduna ba, inji El-Rufai

A bangare guda, gwamnan ya ce bai taba satar kudin talakawa ba tun da ya zama gwamnan jihar Kaduna, kuma zai iya rantsewa da Allah a kan hakan, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Hakazalika, ya yi tsokaci ga irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi da kuma irin tasirin da ayyukan za su yi a nan gaba.

A cewarsa:

“Zan iya rantsewa ban taba satar Kobo a asusun gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Jarrabawa: Bayan mutuwar dansa, Allah ya sake jarabtan gwamnan APC Sule, kaninsa ya rasu

“Na yi farin ciki da abin da muka gani. Ayyukan da muka fara da ingancin ayyukan, za mu kwashe shekaru muna jin dadinsu.”

Ba wannan ne karon farko da gwamnan jihar ta Kaduna ke kalubalantar ‘yan siyasa su rantse game da gaskiyarsu ko akasin haka ba, ya sha yin hakan a baya.

Ban taba sace kudin talaka ba

A tun farko, gwamnan ya yi magana yayin da mulki a Najeriya yake zuwa gangarar shekaru hudu da aka soma kirga a shekarar mulki ta 2019.

‘Yan Najeriya na ci gaba da zargin gungun ‘yan siyasa da azurta kansu tare da sace dukiyar al'umma a kowane mataki na mulki.

Sai dai, El-Rufai ya fito don wanke kansa, inda ya bayyana yadda mulkinsa yake da kuma tasirin gaskiyarsa da rike amanar talaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel