Ba Mu Mu Ka Ba Shi Satifiket Ba – NYSC Ta Jefa Gwamna Mai Jiran Gado a Matsala
- An tabbatar da rashin ingancin takardar shaidar kammala NYSC da Peter Mbah yake amfani da ita
- Birgediya Janar Y. D Ahmed ya bayyana cewa ba hukumar da yake jagoranta ta ba ‘dan siyasar satifiket ba
- Darekta Janar na NYSC ya yi wannan bayani ne a lokacin da ake shirin rantsar da zababben Gwamnan
Abuja - Darekta Janar na hukumar NYSC ta kasa, Birgediya Janar Y. D Ahmed ya yi magana a game da takardar shaidar da ke hannun Peter Mbah.
A rahoton da aka samu daga The Cable, an ji Birgediya Janar Y. D Ahmed ya nuna NYSC ba ta san inda ‘dan siyasar ya samu takarddar shaidarsa ba.
Da aka zanta da shi a gidan talabijin Arise, shugaban hukumar bautar kasan ya shaida takardar bogi Mbah yake amfani da ita a matsayin satifiket.
Sojan ya yi Allah-wadai da yadda manyan mutane su ke amfani da takardar shaida ta bogi a kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da DG NYSC ya fada
"Ya zo wuri na kuma na kira Darekta na domin tabbatar da ingancin satifiket din sai mu ka gano cewa satifiket dinsa na bogi ne, kuma na fada masa…
Ina mamakin yadda manya da suka je makaranta za su koma amfani da takardar shaidar bogi.
Kowa ya san yadda mu ke bada takardar shaidarmu a NYSC, ba mu badawa a otel ko gidaje.
Zababben Gwamnan Lauya ne. Ni ba Lauya ba ne, amma a matsayina na Darekta Janar na NYSC na san da batunsa, ya same ni, na fada masa gaskiya.
- NYSC DG
Magana ta tafi kotu
Ana haka sai ga jaridar Punch ta rahoto cewa Mbah ya shigar da kara a kotu ya na neman hukumar ta NYSC ta ba shi Naira biliyan 20 saboda bata masa suna.
‘Dan takaran ya na ikirarin zargin wannan badakala ta rage masa kima, duk abin da ake yi, Janar Ahmad ya ce NYSC ba ta san an shigar da kararta a kotu ba.
Jam'iyyar PDP ta jefi shugaban NYSC da karya, ta ce takardar shaidar Mbah na gaske ne.
Za ayi sababbin Gwamnoni
A baya an samu labari Bukola Saraki ya bada shawarwarin da za su taimakawa Gwamnoni masu barin gado da masu cin gadonsu a karshen Mayun 2023.
Aminu Tambuwal, Aminu Masari, da Gwamnoni 18 za su fice daga fadar Gwamnati, irinsu Abba Kabir, Dauda Lawal, da Rev Fr Hyacinth Alia za su karbi mulki.
Asali: Legit.ng