Bukola Saraki Ya Ba Gwamnoni Shawarar Yadda Za Su Zauna Lafiya da Magadansu

Bukola Saraki Ya Ba Gwamnoni Shawarar Yadda Za Su Zauna Lafiya da Magadansu

  • Bukola Saraki ya ba Gwamnonin da za su sauka sirrin rayuwa bayan an fice daga fadar gwamnati
  • Tsohon Gwamnan Kwara ya ce da zarar Gwamna ya bar mulki, ya guji yi wa magajinsa shisshigi
  • Wadanda suka yi mulki a baya sun ba Gwamnonin da za su bar gado da masu shigowa shawarwari

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ba gwamnonin da za su bar ofis shawarar su guji yi wa magadansu katsalandan a mulkinsu.

Yayin da gwamnatinsu ta zo karshe, Bukola Saraki ya fadawa gwamnoni 18 masu barin-gado cewa su fara shiryawa rayuwa bayan barin daular gwamnati.

Punch ta ce tsohon Gwamnan na jihar Kwara yana so shugabannin su canza salon rayuwarsu domin su bada irin na su gudumuwar wajen cigaban kasa.

Gwamnoni
Wasu Gwamnoni a Aso Rock Hoto: persecondnews.com
Asali: UGC

A matsayinsa na tsohon Gwamna, an gayyaci Saraki domin ya yi jawabi a wajen liyafar da aka shiryawa wadannan Gwamnoni a wani otel da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana a ranar Lahadi, Dr. Saraki ya jinjinawa Gwamnoni da za su cika wa’adinsu.

Shawarar tsohon shugaban kungiyar gwamnonin kasar na NGF ga gwamnonin da za su dare mulki kuwa shi ne su fara aiki tun daga ranar da suka shiga ofis.

Jawabin Dr. Abubakar Bukola Saraki

"Idan kun sauka daga Gwamna, ku kyale magadanku su yi aikinsu. Ku koma wajen iyalanku, na tabbata mata, ‘ya ‘ya da jikokinku sun fara kirga kwanaki.
Ku na tunkarar sabon babi a rayuwa wanda ya sha bam-bam. Ku rika yawan zama da iyali. Ku adana kudin sayen rago domin an daina samunsu kamar da."
Ga gwamnoni masu hawa mulki, ku fara tsare-tsare, ku na shiryawa shugabanci. Ku shiryawa barin gidan gwamnati tun daga ranar farko.

- Bukola Saraki

Kiran Muazu Babangida Aliyu

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Rahoton ya ce Muazu Babangida Aliyu wanda ya yi Gwamna a jihar Neja ya yi jawabi a taron, ya bada shawarwari, an fada masu su shiryawa EFCC da NFIU.

Ibrahim Dankwambo ya tofa albarkacin bakinsa a gaban Kayode Fayemi, Aminu Tambuwal, Aminu Masari, Charles Soludo da Sanata Bala Mohammed.

Babagana Zulum, Dauda Lawal, Hyacinth Alia da wasunsu sun halarci taron na daren yau.

Gawuna zai mulki Kano a 2023?

Jigon jam'iyya mai-ci, Ahmadu Haruna Dan Zago, ya yi kira ga 'Yan APC su fito daga rudanin jiran a rantsar da Nasiru Gawuna a matsayin gwamnan Kano.

An samu rahoto Ambasada Ahmadu Dan Zago ya ce abin da zai hana a rantsar da Abba Kabir Yusuf a Kano su ne mutuwa ko kuma an yi juyin mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel