Yadda Aka Ji Ganduje a Tarho Yana Kokawa Kan Zaman Tinubu da Kwankwaso a Faransa

Yadda Aka Ji Ganduje a Tarho Yana Kokawa Kan Zaman Tinubu da Kwankwaso a Faransa

  • An ji muryar da ake tunanin Abdullahi Umar Ganduje ne ya tattaunawa da Ibrahim Kabir Masari waya
  • Faifen ya tona maganar da Gwamnan Kano ya yi da na-hannun daman Bola Tinubu a kan siyasar kasa
  • Dr. Abdullahi Ganduje bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya zauna da Rabiu Kwankwaso a Faransa ba

Kano - A wani faifai da ake zargin Abdullahi Umar Ganduje ne ya ke bayani, an ji gwamnan Jihar Kano ya na kuka da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Daily Nigerian ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya kebe a kasar waje tare da abokin gabansa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba.

A faifen mai tsawon minti hudu da yake yawo tun ranar Juma’a, ana tunanin Mai girma Gwamnan na jihar Kano ya kai kukansa wajen Ibrahim Kabir Masari.

Kara karanta wannan

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Aika Bukata a Wajen Tinubu Kafin Ya Shiga Aso Rock

Tinubu da Ganduje
Bola Tinubu da Abdullahi Ganduje a Legas Hoto: www.newsmakerslive.org
Asali: UGC

Gwamnan mai barin-gado ya na ganin zababben shugaban kasar bai kyauta ba, ya ce ya kamata idan za ayi zama irin wannan akalla a gayyato ko domin jama’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdullahi Ganduje ya nuna ba ayi masa adalci ba yayin da Ibrahim Masari yake ba shi hakuri, ya nuna masa ya zo su zauna, bai dace a rika maganar a waya ba.

Dr. Ganduje ya fara da fadawa Masari ana ta surutu a ko ina a Kano a dalilin zaman da Tinubu ya yi da Kwankwaso a Faris, Masari ya ce dama ya san za a rina.

"Saboda mun fadi zabe"

Jaridar ta ce Gwamnan mai barin mulki yake kokawa cewa idan har Tinubu ya na ganin Kwankwaso a madadinsu saboda sun rasa zabe, to babu komai.

A wayar da ake zargi, Dr. Ganduje ya ce Kwankwason da ake zawarci ne ya jawo APC ta fadi zabe a Kano, ya na mai tunawa Masari cewa mulki na Allah ne.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Fadakar da Najeriya a Kan Hadarin da Ake Dosa a Gwamnatin APC

Za a iya jin Alhaji Masari yana lallashin Gwamnan na Kano, ya ce ya yarda ba a kyauta masa ba. Ganduje ya ja-kunne a kan zawarcin tsohon Gwamnan.

Sanusi Lamido Sanusi

A cewar Masari, ya tuntubi Tinubu da ya ji labarin ya zauna da ‘dan adawar ya kuma nuna masa bai kyauta ba, amma Tinubu ya fada masa aikin Sanusi Lamido ne.

Uzurin da Tinubu ya bada shi ne tsohon Sarkin Kano ya yi sanadiyyar hada wannan zama ta hannun Gilbert Chagoury, abin da ya yi wa ‘Yan APC ciwo sosai.

Gwamna bai yi magana ba

Jaridar ta ce ta tuntubi Kakakin Gwamnan, Abba Anwar domin jin gaskiyar zancen, amma bai amsa ba.

Zuwa yanzu ana ta surutu a game da wannan faifai da aka fito da shi a shafukan sada zumunta. Nan da kwanaki tara Abdullahi Ganduje zai sauka daga kan mulki.

Aminu Ado Bayero ya bada shawara

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Duro Najeriya, Ana Jiran Ya Fadi Yadda Suka Yi da Tinubu a Faransa

Kungiyar ActionAid Nigeria ta shirya taro domin hada-kan mabanbanta addinai, an ji labari an gayyaci Mai martaba Sarkin Kano domin ya sa wa taron albarka.

A wajen taron Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba Bola Tinubu shawarar da za ta taimaka masa, ya ce kyau a kafa ma'aikata ta musamman domin kula da addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel