Ni Da Kwankwaso Mun Sayar Da Gidajen Gwamnatin Kano, Ganduje Ga Abba Gida-Gida

Ni Da Kwankwaso Mun Sayar Da Gidajen Gwamnatin Kano, Ganduje Ga Abba Gida-Gida

  • Gwamna Ganduje ya maida martani ga zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf watau Abba Gida-Gida
  • Ganduje ya ce sayar da kadarorin gwamnati ba kansa farau ba, tun a zamanin mulkin Kwankwaso aka fara
  • Gwamnatin Abba Gida-Gida ta sha alwashin gudanar da bincike kan yadda Ganduje ya sayar da kayayyakin gwamnati

Kano - Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso, ce ta fara sayar da kadarorin gwamnatin jihar a lokacin yana mataimakin gwamna.

Ganduje ya faɗi haka ne a wani sautin murya da ke yawo, yayin maida martani kan shirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf mai zuwa na bincikar yadda gwamnatin Ganduje ta sayar da kadarorin Kano.

Gwamna Ganduje.
Ni da Kwankwaso Mun Sayar da Gidajen Gwamnatin Kano, Ganduje Ga Abba Gida-Gida Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa kwamitin karban mulki da zababben gwamna ya kafa, ya gargaɗi injiniyoyi da duk waɗanda suka sayi wata kadara daga hannun gwamnati su dakata da aiki tun yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Fadakar da Najeriya a Kan Hadarin da Ake Dosa a Gwamnatin APC

Kwamitin ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida yana shirin bibiyar yadda aka sayar da waɗan nan kayayyaki da zaran ya shiga Ofis ranar 29 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganduje ya maida martani ga Abba Gida-Gida

Da yake martani ga kalaman gwamna mai jiran gado, Ganduje ya ce sayar da kadarorin gwamnati a Kano ba sabon abu ne, ya koma ya tambayi Uban gidansa a siyasa kan yadda tsarin ya faro.

Ganduje ya rike kujerar mataimakin gwamna Kwankwaso tsawon zango biyu 1999-2003 da 2011-2015 daga baya kuma ya gaje shi. Sai dai sun samu matsala tun a zangon mulkin Ganduje na farko.

A sautin muryar da ke yawo, an ji gwamna Ganduje na cewa:

"Tun a gwamnatin Kwankwaso da Ganduje muka kawo wannan tsarin, mun sayar da gidaje, mafi yawa ga ma'aikata da 'yan siyasa. Suna ta ɓaɓatun mun sayar da gidajen gwamnati ba tare da sun san Kakansu a siyasa ne ya koya mana ba."

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

"Idan kuma ya ƙaryata, ya shiga gidan Radiyo zai samu cikakken jerin gidajen da ubangidansa a siyasa (Kwankwaso) ya sayar. Amma yanzu ba lokacin buɗe wannan shafin bane."
"Idan zan lissafo sunayen manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasar da suka sayi gidajen gwamnati to zamu kwana muna yi amma ba mu kammala ba."

Gwamnan ya ƙara da cewa tsarin sayar da gidajen da gwamnati ta gina ba sabon abu bane, ba yanzu aka fara ba kuma ba yanzun za'a daina ba domin ba laifi bane.

Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Zababben Gwamna

A wani rahoton kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya Ta Soke Halascin Takarar Zababɓen Gwamna da Wasu 'Yan Takara a Kano da Abiya.

Yayin yanke hukunci Kotun mai zama Kano ta ce LP ta karya dokar zabe wajen fidda 'yan takara, don haka baki ɗayansu tikitinsu bai halatta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel