Abinda Ya Janyo Atiku da Peter Obi Suka Sha Kashi a Zaben 2023, Shittu
- Tsohon ministan sadarwa ya bayyana muhimman abu 2 da suka cuci manyan yan takarar adawa, Atiku da Peter Obi
- Adebayo Shittu, ya ce rashin hangen nesa da haɗin kai mai kwari ne ya ja wa PDP da LP shan kaye a zaben shugaban kasa
- Haka nan ya ce da APC ta so yin magudi babu yadda za'ai ta bari wata jam'iyya ta lashe jihar Legas
Abuja - Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Adebayo Shittu, ya ce abu biyu ne suka cuci manyan yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben 2023.
Mista Shittu ya ce Atiku da Obi sun sha ƙasa a zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 saboda rashin hangen nesa da haɗin kai mai ƙarko.
Daily Trust ta rahoto cewa Shittu ya faɗi wannan kalaman ne a wurin taron manema labarai wanda gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan APC suka shirya a Abuja.
A halin yanzun, Atiku da Peter Obi sun nufi Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa, inda suka kalubalanci ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin wanda ya samu nasara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma da yake jawabi ga yan jarida, Shittu ya ce:
"Allah baya bacci kuma yana aiki, Allah ne ya tsara cewa Atiku da Peter Obi ba zasu haɗu wuri ɗaya a matsayin ɗan takarar shugaban kasa da mataimaki ba. Da sun yi haka mu zamu sha ƙasa."
"Amma sam suka gaza hango haka, Wannan gazawa da kayen da suka sha duk sakamako ne na rashin hangen nesansu da kuma tsarin haɗaka mai kwari."
"A zaben 2019, Buhari ya samu kuri'u miliyan 16M, a wannan karon kuma Tinubu ya samu kuri'a miliyan 8m. Tsagin adawa sun rarrabu kashi-kashi shiyasa cikin sauki muka samu nasara."
Shin APC ta yi magudi a zaben 2023?
Da yake tsokaci kan zargin da wasu ke yi cewa an yi maguɗi, Tsohon ministan ya ce kowace jam'iyyar siyasa idan zata yi maguɗi ta kan yi ne a wurin da take da cikakken goyon baya.
"Idan muka ɗauko batun maguɗi, za kai tunanin maguɗi ne a wurin da kake da ƙarfi, wurin da kake da cikakken goyon baya. Manyan jihohin da zamu iya maguɗi Legas ne da Oyo, da wasu wuraren."
"Kowane ɗan Najeriya ya san ba mu muka samu kuri'u mafi rinjaye ba a jihar Legas, to taya zaku ce mun yi magudi?"
El-Rufai Ya Soke Lasisin Hakkin Mallaka Na Kamfanoni 9
A wani labarin kuma Gwamna El-Rufai Ya Waiwayo Kan Kamfanoni 9 na tsohon Gwamnan jihar Kaduna, ya aike musu da Notis.
Yayin da ya rage kwana 10 ya gama mulki, Gwamann ya soke lasisin kamfanonin kana ya buga musu tambarin rsuhewa.
"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru
Asali: Legit.ng