Emefiele Ya Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Aike da Sako Ga Buhari

Emefiele Ya Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Aike da Sako Ga Buhari

  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sake shiga sabuwar matsala yayin da Bello Matawalle ya nemi a hatamta masa hutun da ya nema
  • Matawalle, gwamnan Zamfara kuma jagoran APC a jihar ya nemi shugaba Buhari kar ya aminta da buƙatar Emefiele
  • Ya ce ya zama wajibi a dakatar da Emefiele domin ya yi bayanin duk abinda ya faru a lokacin da ya shafe kan kujerar gwamnan CBN

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya roki shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kar ya aminta da daɗin bakin gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Matawalle ya roki shugaba Buhari kar ya aminta da bukatar tafiya hutun ƙaro karatu wanda gwamnan CBN ya nema, makonni kaɗan kafin rantsar da sabuwar gwamnati.

Buhari da Emefiele.
Emefiele Ya Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Aike da Sako Ga Buhari Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan kira ga shugaban kasa a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

Meyasa Matawalle ya nemi Buhari ya dakatar da Emefiele?

A cewar Bello Matawalle, Gwamnan CBN na neman tafiya wannan hutun ne, "Ba don komai ba sai don ya kauce wa ba da ba'asin harkokin babban banki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan, wanda ya sha kaye hannun PDP a kokarin neman tazarce, ya zargi gwamnan CBN da kitsa aiwatar da tsarin sauya fasalin takardun naira, wanda ya jefa 'yan Najeriya cikin ƙunci.

Haka zalika, sabon tsarin canja takardun kuɗin, wanda Matawalle ya ɗora laifin kitsa tilasta aiwatar da shi kan Emefiele, ya ƙara gurgunta tattalin arzikin ƙasar nan.

Daily Trust ta rahoto Matawalle na cewa:

"Wai wannan Emefielen ne yake neman a sahale masa ya tafi hutu a lokacin da ya rage masa watanni 10 wa'adinsa ya ƙare, a zahiri ya na son guduwa ne kar ya yi bayani."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

"Wannan ba zata sabu ba, bai kamata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan ba, shi mutum ne mai gaskiya da kwatanta adalci."

Menene gaskiya kan batun tafiya hutun gwamnan CBN?

Har yanzun a tsakanin Emefiele da CBN babu wanda ya fito ya karyata raɗe-raɗin wannan hutun da ake zargin Emefiele na yunkurin tafiya.

A halin yanzu gwamna Matawalle ya jaddada cewa ya zama tilas Emefiele ya jira ya ba da bayani dalla-dalla kan duk abinda ya faru karkashin mulkinsa a CBN.

A wani rahoton kun ji cewa Sabon Rikici Ya Barke a APC Kan Zaben Shugaban Kasa 2023 Wanda Aka Kammala

Wasu masu ruwa da tsaki sun tuhumi shugaban jam'iyya na shiyyar arewacin jihar Edo na yin sama da faɗi da kuɗin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel