Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima

Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima

  • Mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, Kashim Shettima, ya faɗi dalilin APC na zaben shugabannin majalisa
  • Shettima ya ce APC ba zata so shiga cikin raɗe-raɗin ana kokarin Musuluntar da Najeriya ba
  • Ya ce ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen rarrashin sauran yan takara su hakura su marawa zabin jam'iyya baya

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon gwamnan Akwa Ibom, Godwill Akpabio a matsayin ɗan takarar da take goyon bayan ya zama shugaban majalisar dattawa saboda daidaiton addini da kishin ƙasa.

Zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Ƙashim Shettima, ne ya bayyana haka ranar Jumu'a 12 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda The Nation da rahoto.

Kashim Shettima da Yan Majalisa.
Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima Hoto: Hon. Banjemin Kalu/facebook
Asali: Facebook

Meyasa APC ta zabi Abbas a majalisar wakilai?

Ya ce Najeriya da jam'iyyar APC ba zasu aminta a shiga yanayin da za'a ce manyan shugabanni huɗu na farko a ƙasar nan duk mabiya addinin ɗaya ne.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shettima ya yi wannan karin haske sa'ilin da 'yan majalisar APC suka je neman goyon bayan tikitin Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu, a matsayin kakaki da mataimakin kakakin majalisar wakilai ta 10.

Yayin ganawa da yan majalisun a Abuja, Shettima ya ce APC ba zata yarda ta shiga sahun gaba a raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa ana shirin maida Najeriya ƙasar Musulunci.

Ya jaddada cewa samun kwanciyar hankali da daidaito a Najeriya ya fi muhimmanci fiye da burikan siyasa, kamar yadda This Day ta rahoto.

Zamu rarrashi sauran yan takara - Shettima

Zababben mataimakin shugaban ƙasan ya ƙara da cewa APC zata ci gaba da rarrashin waɗanda suka fusata kan mutum huɗun da ta zaɓa su jagoranci majalisar tarayya ta 10.

Ya ayyana Abbas da, "Kakakin majalisa mai jiran gado idan Allah ya so," da kuma kalu, "mataimakin kakakin mu mai jiran gado."

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

"Zan yi bakin kokari na rarrashi sauran yan takara su yi hakuri, Honorabul Betara ɗan uwana ne, yankinmu ɗaya, jiharmu ɗaya kuma akwai alaka mai kyau a tsakaninmu, mun haɗu shekaran jiya, zan kara rarrashinsa."
"A yau (Jumu'a) na gana da mataimakin kakakin majalisa, Honorabul Ahmed Wase. Zamu ci gaba da zama muna kara rarrashinsu domin komai ya tafi cikin ruwan sanyi a majalisa."

- Kashim Shettima.

Mahmud Yakubu Ya Yi Aiki Karkashina Kafin Zama Shugaban INEC - Peter Obi

A wani labarin kuma Peter Obi ya bayyana yadda shugaban INEC ya yi aiki a karkashinsa a baya

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya ce Farfesa Mahmud Yakubu, tsohon yaronsa ne lokacin da suka yi aiki a kwamitin TETFUND.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262