Majalisa Ta 10: Yari, Kalu da Sauran Fusatattun Yan Takara Sun Gana da Shugaban APC

Majalisa Ta 10: Yari, Kalu da Sauran Fusatattun Yan Takara Sun Gana da Shugaban APC

  • Fusatattun sanatocin APC da ke neman kujerar shugaban majalisar dattawa sun gana da Adamu, mambobin NWC
  • Sanata Abdul'aziz Yari, ya gabatar da wasiƙar koken 'yan takara ga Sanata Abdullahi Adamu, shugaban APC
  • Sanata Kalu ya ce abinda uwar jam'iyya ta ƙasa ta duba wajen raba muƙaman majalisa bai dace ba

Abuja - Fusatattun Sanatocin jam'iyyar APC da ke neman kujerar shugaban majalisar dattawa sun gana da mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na jam'iyyar APC a Abuja.

Channels tv ta tattaro cewa Sanatocin da suka halarci taron sun haɗa da, Abdul'Aziz Yari, Orji Kalu, Muhammed Musa da Sadiq Umar.

Majalisa ta 10.
Majalisa Ta 10: Yari, Kalu da Sauran Fusatattun Yan Takara Sun Gana da Shugaban APC Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

Shugaban APC, Abdullahi Adamu, Sakatare na ƙasa, Iyiola Omisore; da shugabar matan APC ta ƙasa, Beta Edu, sun halarci taron wanda ya gudana hedkwatar jam'iyya da ke Abuja.

Da yake jawabi ga kwamitin NWC, Sanata Kalu, ya ce a duk lokacin da aka baiwa kowane shiyya haƙkinsa yana kara ɗaga komaɗar Najeriya ta yi kyau.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bai kamata APC ta tsoma baki ko ta raba muƙaman majalisar tarayyan da ba'a kai ga rantsarwa ba bisa la'akari da yawan kuri'un da kowace shiyya ta baiwa zababben shugaban kasa.

Sanata Kalu ya ƙara da cewa zata iya yuwuwa shiyyar da aka raina saboda ta ba da kuri'u yan kaɗan a zaben da ya gabata, ta kawo tulin kuri'a a babban zaɓe na gaba.

Yari ya miƙa wasiƙa ga shugaban APC na ƙasa

A wurin taron, Sanata Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya gabatar da wasiƙar da fustattun zababbun sanatoci suka rubuta kokensu zuwa shugaban jam'iyyar APC.

Bayan nan, Sanata Yari ya roki APC ta sake nazari kan jadawalin raba kujerun majalisar tarayya wanda ta fitar kwanaki kaɗan da suka shige domin kwatanta adalci da daidaito.

Idan baku manta ba a ranar Linin, APC ta fitar da jadawalin shiyyoyin da zasu samar da shugabannin majalisar tarayya ta 10.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Mai Jiran Gado, Bola Tinubu Zai Ƙara Tafiya Ƙasar Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Daga ciki, APC ta zaɓi Sanata Godwill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar dattawa (shiyyar kudu maso kudu) da Sanata Barau Jibrin, a matsayin mataimaki (arewa ta yamma).

Dan majalisa ya sauya sheƙa zuwa PDP

A wani labarin kuma Bayan Shan Kaye a Babban zaben 2023, Dan Majalisar Tarayya Ya Koma Jam'iyyar PDP

Wani ɗan majalisar tarayya a jihar Delta, wanda ya tattara kayansa ya bar PDP saboda hana shi tikitin tazarce, ya sake komawa jam'iyyar bayan gama zaɓen 2023.

A cewarsa, kudi ne suka yi sanadiyyar hana shi komawa majalisar tarayya a zaben da aka kammala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel