Atiku, Obaseki da Wasu Gwamnonin PDP Sun Halarci Babban Taro a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya halarci taron da PDP ta shirya wa zababbun gwamnoni
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, takwaransa na jihohin Taraba da Adamawa suna cikin waɗanda suka isa a kan lokaci
- Ana tsammanin baki ɗaya gwamnoni masu jiran gado, zababbu da waɗanda suka zarce zasu hallara a wurin
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023 da wuce, Alhaji Atiku Abubakar, ya halarci taron liyafa da aka shiryawa zababbun gwamnonin PDP a Abuja.
Punch ta ce gwamnonin da suka fara dira wurin taron da wuri sun haɗa da gwamnan Edo, Godwin Obaseki, takwaransa na Taraba, Darius Ishaku, da Ahmadu Fintiri na Adamawa.
Ana sa ran taron, wanda aka shirya gudanawa yau Alhamis 11 ga watan Mayu, 2023 a Transcorp Hilton, Abuja, zai haɗa jiga-jigan jam'iyyar PDP daga kowane bangare.
Cikin waɗanda yanzu haka suka nemi wuri suka zauna a wurin liyafar sun haɗa da toshon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, da Tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka zalika an hangi muƙaddashin shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Sanata Adolphus Wabara da wasu jiga-jigai sun nemi wuri sun zauna.
Bugu da ƙari, babban bako mai jawabi, Mudal Yusuf, zai yi lakca kan maudu'i mai taken, "Shugabanci nagari a matakin jihohi: Batutuwa, tsammani da sakamakon da ake sa rai."
Mai yuwuwa Atiku da Wike su haɗu a wurin
Ana tsammanin wannan liyafa ta musamman ka iya haɗa ƙusoshin jam'iyyar PDP masu adawa da juna a karon farko tun bayan kammala babban zaɓen 2023.
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na cikin gwamnonin PDP masu barin gado da ake tsammanin zasu halarci taron, kuma da yuwuwar ya haɗu da Atiku, abokin faɗansa a cikin gida.
A wani labarin kuma kun ji cewa Yari, Kalu da Sauran Fusatattun Yan Takarar Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa Sun Gana da Shugabannin APC
Sanatocin sun gabatarwa Abdullahi Adamu wasiƙar kokensu kan wanda zai gaji Sanata Ahmad Lawan a majalisar tarayya ta 10.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta sanar da sunan Sanata daga kudu maso kudu a matsayin wanda take goyon baya.
Asali: Legit.ng