Jam'iyyar APC Da Dakatar Da Tsohon Minista Da Wasu Manyan Jiga-jiganta a Jihar Benue

Jam'iyyar APC Da Dakatar Da Tsohon Minista Da Wasu Manyan Jiga-jiganta a Jihar Benue

  • Jam'iyyar APC a jihar Benue ta dakatar da wasu manyan ƙusoshinta a jihar, bisa zargin ci mata dunduniya
  • Jam'iyyar ta dakatar da tsohon ministan ayyuka, Barnabas Gemade, da Farfesa Terhemba Shija daga cikinta
  • Jam'iyyar na zargin su Gemade da haɗa baki da jam'iyyar PDP domin ganin ta faɗi zaɓen gwamnan jihar, bayan sun sha kashi a zaɓen fidda gwani

Jihar Benue - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Benue, ta dakatar da tsohon ministan ayyuka, Barnabas Gemade, daga jam'iyyar bisa zargin yi mata zagon ƙasa.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa, shugaban jam'iyyar na jihar, Austin Agada, shine ya bayyana hakan, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ranar Laraba, a birnin Makurdi, babban birnin jihar.

Jam'iyyar APC ta dakatar da Barnabas Gemade
Barnabas Gemade, tsohon ministan ayyuka kuma jigo a jam'iyyar APC Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Mr Agada ya bayyana cewa jam'iyyar ta kuma dakatar da Terhemba Shija da wasu shugabanninta na wasu mazaɓu, bisa zargin cewa sun ci dunduniyarta lokacin babban zaɓen 2023.

Jaridar Tribune tace, Gemade da Shija ƴan takarar gwamnan jam'iyyar a zaɓen fidda gwani, wanda Hyacinth Alia ya lashe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa bayan kai ƙarar jam'iyyar kotu, Gemade wanda tsohon sanata ne, da Mr Shija wanda farfesa ne, sun yi wa jam'iyyar zagon ƙasa domin ganin ta faɗi zaɓe.

A kalamansa:

"Gemade ya yi rashin nasara a rumfar zaɓensa, mazaɓarsa da ƙaramar hukumarsa a hannun jam'iyyar adawa, yayin da Shija ya haɗa baki da jam'iyyar PDP."
"Har yanzu Shija yana kotu sannan yana aiki kafaɗa da kafaɗa tare da jam'iyyar PDP, domin ganin kotu ta ƙwace nasarar Alia ya samu a zaɓen gwamnan jiha."

Shugaban jam'iyyar ya kuma bayyana cewa an miƙa lamarin hannun, kwamitin bin ƙwaƙwaf na jam'iyyar, domin gano dalilan da za su sanya ba a kore su daga jam'iyyar ba.

Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

Da zu rahoto ya zo cewa, ƴan takarar kujerun shugaɓancin majalisa sun gana da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.

Fusatattun ƴan takarar sun ce sam ba su amince da matsayar jam'iyyar ba, kan shugabancin majalisa ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel