Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Sanar Da Wadanda Za Su Shugabanci Majalisa Ta 10

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Sanar Da Wadanda Za Su Shugabanci Majalisa Ta 10

  • Jam'iyyar APC ta sanar da Sanata Godswill Akpabio, zaɓaɓɓen sanata daga jihar Akwa Ibom, cewa shine ɗan takararta a shugabancin majalisar dattawa ta 10
  • Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC, a wata sanarwa ranar Litinin, ya kuma sanar da zaɓar Abbas Tajudeen, a kujerar kakakin majalisar wakilai
  • Yankin Arewa maso Yamma ya samu mataimakin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai, yayin da yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas suka samu shugaban majalisar dattawa da mataimakin kakakin majalisa

Abuja - Jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta bayyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda ta zaɓa ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Haka kuma, jami'iyyar ta zaɓi Abbas Tajudeen, ɗan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, a matsayin wanda zai zama kakakin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Kori Karar Jam'iyya 1 Daga Cikin Waɗanda Suka Kalubalanci Nasarar Tinubu

APC ta sanar da zabin ta a shugabancin majalisa ta 10
Bola Tinubu da shugaba Buhari a wajen kamfe Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Jami'iyyar APC dai har yanzu itace ta ke ƴan majalisu masu rinjaye a majalisar dokoki ta tarayya.

Kakakin jam'iyyar na ƙasa, Felix Morka, shine ya bayyana zaɓin jam'iyyar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 8 ga watan Mayun 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugaban majalisar wakilai, yankin Kudu maso Kudu - Sanata Godswill Akpabio (jihar Akwa Ibom), mataimakin shugaban majalisar dattawa, yankin Arewa ta Yamma - Sanata Barau Jubrin (jihar Kano)."

Sanarwar ta kuma nuna cewa yankin Arewa maso Yamma ya samu kujerar kakakin majalisar wakilai, domin Abbas Tajudeen ya fito daga jihar Kaduna, yayin da yankin Kudu maso Gabas, ya samu kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai, inda Benjamin Kalu ya fito daga jihar Abia.

Morka ya ƙara da cewa wannan sabon tsarin na jam'iyyar ya samu ne a dalilin taron da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar ya yi, da la'akari da taron da aka yi da Bola Tinubu, da wasu manyan ƙusoshi kan yadda za a raba kujerun majalisar ta 10.

Kara karanta wannan

Sabon Sanata Zai Birkita Lissafi Ya Fado Cikin Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Sabon Sanata Zai Birkita Lissafi Ya Fado Cikin Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

A wani rahoton kuma, sabon sanata ya shiga cikin jerin sahun masu son ɗarewa kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Sanata Patrick Ndubueze, ya sanar da jam'iyyar APC a hukumance, aniyarsa ta neman kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel