Peter Obi, Atiku Abubakar, Ayu da Gwamna Makinde Sun Hadu a Wurin Jana'iza

Peter Obi, Atiku Abubakar, Ayu da Gwamna Makinde Sun Hadu a Wurin Jana'iza

  • Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP a babban zaɓen 2023 ya haɗu da takwaransa na Labour Party, Peter Obi, a wurin jana'izar mahaifin gwamnan Bayelsa
  • An hangi manyan 'yan takarar da suka nemi kujerar shugaban ƙasa tare da tsohon shugaban PDP, Iyorchia Ayu, da gwamna Seyi Makinde na Oyo
  • Wasu masu sharhi sun ce sauya shekar Peter Obi daga PDP zuwa LP da rigimar gwamnonin G-5 ne suka lalata damar Atiku a 2023

Bayelsa - Da alamu jam'iyyar PDP da ta wargatse ta kama hanyar tattaro bangarorinta domin sake haɗewa wuri ɗaya bayan an ga fusatattun mambobinta sun haɗu da juna.

Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a babban zaben 2023, ya gana da takwaransa na Labour Party, Peter Obi, a wurin bikin binne mahaifin gwamnan Bayelsa.

Kara karanta wannan

Rigimar Cikin Gida Ta Sake Dawowa, Shugaban PDP Na Ƙasa, Ayu Na Tsaka Mai Wuya

Bikin jana'iza.
Peter Obi, Atiku Abubakar, Ayu da Gwamna Makinde Sun Hadu a Wurin Jana'iza Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Vanguard ta tattaro cewa manyan jiga-jigan siyasan biyu sun haɗu a wurin Jana'izar wanda ta gudana ranar Asabar 6 ga watan Mayu, 2023.

Meya haɗa Atiku, Obi, Ayu, Makinde da wasu kusoshin PDP wuri ɗaya?

Haka nan gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ziyarci jihar mai arzikin Man Fetur domin jajantawa gwamna Douye Diri, kuma an hange shi zaune a gefen Atiku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, wanda ya sauka daga kan muƙaminsa bisa umarnin Kotu, Dakta Iyorchia Ayu, ya halarci wurin bikin jana'izar.

Tun kafin babban zaɓen 2023, Peter Obi, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa LP gabanin zaben fidda gwani, inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party.

Rigimar gwamnonin G-5

Sai dai ganin gwamna Makinde ya halarci wurin, mamban G-5 wanda ya yaƙi burin Atiku na zama shugaban ƙasa a babban zaben da ya wuce, ya baiwa mutane mamaki.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, PDP Ta Gudanar da Zabe, Ta Sanar da Sabon Shugaban Jam'iyya da Sakatare a Jiha 1

Idan baku manta ba Makinde da sauran gwamnonin G-5 sun buƙaci mulkin Najeriya ya koma kudu a inuwar PDP, amma fafutukarsu ba ta samu shiga ba a wurin shugabannin jam'iyyar.

Masana da masu sharhi kan siyasa sun ce ficewar Obi daga PDP da rigimar gwamnonin G-5 sun taka rawa wajen ruguza damar Atiku ta zama shugaban ƙasa fiye da komai.

Mista Obi, tsohon gwamnan Anambra ya tabbatar da cewa ya halarci jana'izar a shafinsa na Tuwita.

Tinubu ya taya Sarki Charles III murna

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Aika Wasika Ta Musamman Ga Sabon Sarkin Ingila, Sarki Charles III

Zababben shugaban kasa a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya taya Sarki Charles III bisa naɗinsa a hukumance ranar Asabar.

Shugaba mai jiran gado ya ce a shirye yake su fara aiki tare kuma ya masa addu'ar Allah ya ja da zamaninsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262