"Ba Ni Da Laifa Sai Kotu Ta Tabbatar": Tuhumar Kisa Da Ake Min Ba Zai Hana Ni Neman Mukami Ba, Ado Doguwa

"Ba Ni Da Laifa Sai Kotu Ta Tabbatar": Tuhumar Kisa Da Ake Min Ba Zai Hana Ni Neman Mukami Ba, Ado Doguwa

  • Alhassan Doguwa ya bayyana cewa tuhumar da ake mi shi ba za ta hana shi neman ko wane irin muƙami ba
  • Doguwa ya ce mutanen shi sun gamsu cewa ba shi da laifi shi ya sa su ka ƙara zabar shi
  • Ya bayyana cewa shi fa ba mai laifi ba ne tunda kotu ba ta ayyana shi a hakan ba

FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Najeriya Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa zarge-zargen da ake mishi na kisan kai ba za su hana shi neman takarar shugabancin kujerar majalisar dokoki ba.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, Doguwa ya bayyana hakan ne dai yau Laraba a Abuja a yayin da ya ke bayyana aniyar shi ta neman wannan kujera ta kakakin majalisa, wacce ita ce kujera ta hudu mafi girma a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

Ado Doguwa
Ado Doguwa ya ce shi mai gaskiya ne a yanzu har sai kotu ta tabbatar ya aikata laifi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Doguwa ya ce shi mai biyayya ne sau da ƙafa ga jam'iyyar APC

Mamban wanda yake wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da ke jihar Kano ƙarƙashin jam'iyya mai mulki ta APC ya ce shi ma fa ya cancanta kuma wannan lokaci ne da ya kamata ya riƙe kujerar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Doguwa ya ƙara da cewa shifa dan jam'iyya ne mai biyayya ga uwar jam'iyya a saboda haka ya kamata a ba shi dama ya jagoranci zauren majalisar na 10.

“Ina ƙarƙashin dokar da ke cewa wanda ake tuhuma ba mai laifi bane har sai in kotu ta tabbatar, saboda haka babu wani abu da zai hana ni neman duk wani matsayi da nake ganin na cancanci in nema.
“Ina son ƙara jaddada mu ku cewa babu yadda za a yi ace lallai mutum ya aikata wannan laifi mai girma kuma ya je zaɓen zagaye na biyu kuma har ya yi nasara," in ji Doguwa.

Kara karanta wannan

Kujerar Kakaki: Ado Doguwa Ya Ce Mata 4 Da 'Ya'ya 28 Yake Dashi, Zai Iya Ji da Majalisa

Mutanen mazaɓata sun gamsu da irin wakilci da nake musu

Ya ƙara da cewar yayi nasara duk da ba a karamar hukumar shi aka gudanar da zaɓen zagaye na biyun ba, wanda hakan ke nuni da cewa mutanen mazaɓar shi sun tabbatar da cewa bai aikata laifin kisan kan da ake tuhumar shi da shi ba.

Ya ce:

“Na je da kai na wajen mutanen Tudun Wada na kuma gabatar da kaina, inda na roƙi mutane 7,000 da za su yi zabe, waɗanda kuma su ka yanke cewa lallai sun aminta wannan mutumin ya ci gaba da wakiltar su.”

A rahoton jaridar Vanguard, Doguwa ya kuma ƙara da cewa ya na ganin tikitin Muslim-Muslim na Tinubi da Shetima kamar wani zakaran gwajin dafi ne da su ka gwada kuma su ka ga yadda 'yan Najeriya su ka gudanar da zabin su bisa abin da su ke ganin shi ne daidai a gare su.

Kara karanta wannan

"Na Gaji": Wata Yar Najeriya Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurensu, Sannan Ta Damƙa Mata Motocci Da Gidajen Mijinta

Alhassan Ado Doguwa ya samu ƙuri'u 41,573 a zaɓen da ya gabata wanda hakan ya ba shi nasarar doke abokin gwabzawar shi Yushau Salisu na jam'iyyar NNPP wanda ya samu kuri'u 34,831.

Wata mata ta nemi kotu ta mallaka ma ta kadarorin mijinta

A wani labarin na daban kuma, wata mata ta roƙi kotu ta hannan ta ma ta kadarorin mijin ta da suka haɗa da gidan da su ke ciki da kuma motocin da ya mallaka.

Matar ta roƙi kotu waɗannan buƙatu ne kuma bayan ta nemi kotun da ta raba auren na ta da mijin na ta saboda a cewar ta ta gaji da ci gaba da zaman auren da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel