"Zan Kwato Nasara Ta a Kotu" Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa Ya Sha Alwashi

"Zan Kwato Nasara Ta a Kotu" Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa Ya Sha Alwashi

  • Ɗan takarar gwamnan APC a jihar Bauchi ya zaɓen da ya gabata ya nuna ƙwarin guiwar sa kan ɓangaren shari'a
  • Saddique Baba Abubakar ya ce yana sa ran ɓangaren na shari'a zai masa adalci wajen dawo masa da nasarar sa
  • Abubaƙar ya nuna godiyar sa ga magoya bayan APC bisa juriyar da suka nuna kan abubuwan da suka biyo bayan zaɓen

Jihar Bauchi - Ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen da ya gabata, Amb Saddique Baba Abubakar, ya nuna ƙwarin guiwar sa kan cewa zai kwato haƙƙin sa a kotu.

Da ya ke magana da ƴan jarida ranar Litinin a filin tashi da saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Sir Abubakar Tafawa, jim kaɗan bayan dawowar sa, ya ce yana da fata mai kyau akan ɓangaren shari'a, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: An Hana Daruwan Dalibai 'Yan Najeriya Tsallakawa Zuwa Kasar Egypt, Dalilai Sun Bayyana

Dan takarar gwamnan APC a Bauchi na fatan samun nasara a kotu
Dan takarar gwamnan APC a jihar Bauchi, Abubakar Saddique Baba Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

A kalamansa:

"Mu na saran cewa Allah zai sanya ɓangaren shari'a ya kwato mana nasarar mu Insha Allah."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina son yin amanna cewa ɓangaren shari'a na ƙasar nan abin yarda ne, sannan ina da tabbacin cewa a ƙarshe, za mu dawo da nasarar mu da aka ƙwace. Mu na dawo da nasarar mu, za mu yi wa mutane alƙwarin abinda za mu ba tare da ɓata lokaci ba."

Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC za ta cigaba da zama gagarabadau ba a jihar Bauchi kawai ba, har a faɗin ƙasar nan, inda ya roƙi ƴaƴan jam'iyyar da su cigaba da goya mata baya a kowane mataki, rahoton Independent ya tabbatar.

"Ina son miƙa godiya ta musamman ga ƴaƴan jam'iyyar APC a jihar Bauchi, bisa haƙurin su da fahimtar su duba da abinda ya auku bayan zaɓe. Ina roƙon su da su cigaba da haƙuri da fatan nasara."

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Rantsuwa, Firaministan Ingila Ya Waiwayo Kan Bola Tinubu, Ya Fadi Shirin Ingila Kan Gwamnatinsa

Ɗan takarar gwamnan ya bayar da tabbacin cewa, a shirye ya ke ya cigaba da fafutuka a kotu domin ganin ya kwato nasarar sa, saboda a cewar sa da shi da jam'iyyar APC, sun lashe zaɓen gwamnan jihar kuma a shirye yake ya tabbatar da hakan a kotu.

Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

A wani rahoton na daban kuma.kun ji cewa Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ya shiga tseren neman shugaban majalisar wakilai ta tarayya.

Ado doguwa wanda ya ke fuskantar zargin kisan kai a kansa, ya zama mutum na 11 cikin masu neman shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel