Sama Da Dalibai 500 'Yan Najeriya Sun Makale a Iyakokin Sudan Da Egypt

Sama Da Dalibai 500 'Yan Najeriya Sun Makale a Iyakokin Sudan Da Egypt

  • Ɗalibai ƴan Najeriya da ake kwasowa daga ƙasar Sudan na cikin halin tsaka mai wuya a tafiyar su
  • Ɗaliban suna dab da isowa bakin iyakar ƙasar Sudan da Egypt amma ba za su samu tsallakawa ba
  • An zargi hukumomi da yin riƙon sakainar kashi da lamarin kwaso ɗaliban, inda suma gaza yin abinda ya dace

Sudan - Sama da ɗalibai yan Najeriya 500 da ake kwasowa daga Khartoum babban birnin Sudan zuwa ƙasar Egypt, suka maƙale a iyakokin Arewa da Yamma na ƙasasahen biyu, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Sama da mutum 100 daga cikin su suna cikin wani ƙauye mai suna Wadi Halfa, mai nisan ƙasa da kilomita 100 daga ƙasar Egypt saboda kuɗin mota.

Sama da dalibai 500 'yan Najeriya sun makale a bakin iyakar Sudan da Egypt
Wasu daga cikin dalibai na kokarin shiga mota Hoto: Tribune
Asali: UGC

An tattaro cewa jakadan Najeriya na Eguyt da sauran jami'ai suna bakin iyakar domin tarbar ɗaliban, amma ba su samu sun tsallaka ba a daren jiya.

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

"Babu ɗalibi ɗan Najeriyan da ya tsallaka zuwa Egypt. Sudan ta ƙi bari su fita daga ƙasar. Suna karɓar $400 akan kowace mota sannan $10 kan kowane mutum ɗaya." A cewar wata majiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma ƙara samo cewa a yayin da Egypt ta ke neman ganin iznin tsallaka wa zuwa ƙasar ta, sojojin Sudan suna ta tatse ƴan kuɗaden ɗaliban.

"Wasu sun tsallaka da kan su zuwa Saudiyya ta hanyar tashar jirgin ruwan Sudan." A cewar wani mahaifi.

Ɗaliban da ke a ƙauyen Wadi Halfa an dai watsar da su ne a cikin fili, inda su ke ta kwana a ƙasa

A wani faifan murya da aka turo, wata majiya wanda ta san yadda abubuwan ke tafiya, ta bayyana cewa rashin yin aiki a tare na hukumomin da abin ya shafa, shi ya haifar da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Shugaba Buhari Ya kasa Cika Wasu Alkawuran Da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya

Wani majiya ya yi zargin cewa, rashin cimma yarjejeniya da hukumomin Najeriya suka yi da takwarorin su na Egypt, domin samun izinin ɗaliban su shigar mu su ƙasa, wanda hakan ya ke kawo babban ƙalubale ga aikin kwaso su.

"Yanzu da su ke ƙasa da kilomita 100 zuwa Egypt, amma ba za a bari su shiga ba saboda babu wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Egypt. Mutum 7 daga cikin su suna cikin mawuyacin hali, sannan a yanzu haka suna buƙatar tallafi. An aje su ne kawai a wani ƙauye inda babu asibiti, ba abinci." A cewarsa.

A halin da ake ciki, ragowar ɗaliban da ba a kwaso ba daga Khartoum, majiyar ya bayyana cewa sun samu tsaikon tasowa ne sabosa ba a biya kuɗin motocin su ba.

Gwamnatin Buhari Ta Fadi Dalilin Kashe $1.2m Don Kwaso ’Yan Kasar Daga Sudan

A wani rahoton na daban kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan ta na kashe $1.2m domin kwaso ƴan Najeriya daga ƙasar Sudan.

Rikici dai ya ɓarƙe a ƙasar Sudan kan rigimar mulki wands hakan, ya tilasta kasashe kwaso ƴan ƙasar su da rikicin ya ritsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel