Daga Dawowarsa, Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Fara Sintiri Zuwa Wajen Tinubu
- Siyasa ta fara daukar salo bayan dawowar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu daga kasar waje a makon nan
- Shugabannin APC da kusoshi a majalisa da wasu masu neman takara sun ziyarci gidan Bola Ahmed Tinubu
- Barau Jibrin da Godswill Akpabio da za su kara a majalisar dattawa sun gana da shugaba mai jiran gado
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya zauna da wasu daga cikin masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa a majalisa ta goma da za a rantsar a Yuni.
Rahoton Daily Trust ya tabbatar da zababben shugaban na Najeriya ya hadu da manyan Sanatoci irinsu Godswill Akpabio da Barau Jibrin a gidansa.
Ba za a iya cewa ga wainar da aka toya a wajen wannan zama da aka yi a yammacin Talata a Abuja ba, amma da alama ba zai wuce neman kamun kafa ba.
Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila su na cikin wadanda aka zauna da su.
Sanatocin APC sun je gidan Tinubu
Rahoton ya nuna akwai Gwamnonin jihohin Ogun da Ekiti da su Sanata Olamilekan Adeola, Sanata Opeyemi Bamidele da kuma Sanata Emmanuel Bwacha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan Legas ta gabas, Tokunbo Abiru, mataimakin shugaban APC, Abubakar Kyari da James Faleke su na cikin mutanen da aka kebe da su a gidan Tinubu.
Wata majiya ta shaida cewa makasudin zaman shi ne a fito da yadda za ayi rabon kujerun majalisar tarayya tsakanin bangarorin Kudu da na Arewacin kasar.
Tseren Majalisa ta 10
Da yake magana da manema labarai bayan an kammala tattaunawar, Sanata Godswill Akpabio ya nuna shi ya cancanci ya jagoranci majalisar dattawa.
A wani rahoton, an ji Sanatan Arewacin Kano, Barau Ibrahim Jibrin yana mai farin cikin dawowar Tinubu wanda ya shafe tsawon fiye da wata guda a ketare.
Punch ta ce Tanko Almakura da Sanata Barnabas Gemade su na cikin wadanda aka hango a Asokoro.
Ana kishin-kishin cewa jam’iyyar APC mai mulki za tayi kokarin fito da shugaban majalisar dattawa ne daga Kudu maso kudu ko kuwa Kudu maso gabas.
Takarar majalisa a 2023
Ana da labari wasu Gwamnoni da suka yi mulki a Akwa Ibom, Ebonyi, Edo, da Zamfara su na neman kujera #3 a kasa watau shugaban majalisar dattawa.
Alamu na nuna Orji Uzor Kalu da Godswill Akpabio da wani tsohon gwamnan Zamfara za su nemi takara a majalisa idan abubuwa sun tafi masu daidai.
Asali: Legit.ng