Sunayen Tsofaffin Gwamnonin Jihohi Masu Lissafin Zama Shugaban Sanatoci a Bana

Sunayen Tsofaffin Gwamnonin Jihohi Masu Lissafin Zama Shugaban Sanatoci a Bana

  • Akwai tsofaffin Gwamnonin kasar nan da za a rantsar a kujerar Sanatoci nan da watan Yuni
  • Wasu daga cikinsu sun kwallafa rai wajen karbe shugaban majalisar dattawa a majalisa ta goma
  • Wannan karo an saba al’ada, har da sababbin shiga majalisar kasar ake neman takarar shugabanci

Abuja - Tsofaffin Gwamnoni sun saba yin ritaya a majalisar dattawa a siyasar kasar nan, babban zaben da aka yi a 2023 bai zo da wani bambamci sosai ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci inda aka sha bam-bam shi ne duk Sanatocin da suka nemi takarar Gwamna ba su yi nasara ba, Sanata Uba Sani kadai ya ci zabe.

Wani rahoto na Punch ya nuna akwai tsofaffin Gwamnoni 12 da za rantsar a majalisar dattawa.

Wasu daga cikin wadannan tsofaffin Gwamnoni da suka yi mulki a jam’iyyun APC.

Kara karanta wannan

Allah Ya Kawo Mu: Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game Da Ƙaramar Sallah

Gwamnoni a jiya, Sanatoci a yau

A cikin manyan ‘yan siyasar akwai wadanda sun saba da majalisar tarayya, sannan akwai wadanda a 2023 za a rantsar da su a matsayin Sanatoci a karon farko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga jerin nan kamar haka:

Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan a Majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

1. Ibrahim Dakwambo (PDP, Gombe ta Kudu)

2. Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa)

3. Abdulaziz Yari (APC, Zamfara ta Yamma)

4. Orji Uzor Kalu (APC, Abia ta Arewa)

5. Gbenga Daniel (APC, Ogun ta Gabas)

6. Godswill Akpabio (APC, Akwa ta Arewa maso yamma)

7. David Umahi (APC, Ebonyi ta Kudu)

8. Danjuma Goje (APC, Gombe ta Tsakiya)

9. Aliyu Magatakarda Wamakko (APC, Sokoto ta Arewa)

10. Adamu Aliero (PDP, Kebbi ta Tsakiya)

11. Seriake Dickson (PDP, Bayelsa ta Yamma)

12. Aminu Waziri Tambuwal (PDP, Sokoto ta Kudu)

Masu neman shugabanci

Orji Uzor Kalu, Godswill Akpabio, David Umahi su na cikin wadanda ake tunanin za su nemi takarar shugaban majalisa a zaben da za ayi a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Sanatocin PDP Guda 6 Waɗanda Ka Iya Neman Babban Mukami a Majalisar Dattawa

Rahoton ya ce akwai Adams Oshiomhole da Abdulaziz Yari a masu neman mulki a majalisa. Ragowar su ne Orji Kalu, Godswill Akpabio da David Umahi.

Legit.ng Hausa ta fahimci magoya bayan tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun kwallafa rai a wannan kujera duk da su na jam’iyyar PDP.

Alu ya cancanta

Sahabi Sufyan, daya daga cikin matasan APC ya shaidawa Legit.ng Hausa Aliyu Wammako ya cancanci rike majalisar dattawa saboda rawar da ya taka.

Baya ga cewa da shi aka kafa APC, Sahabi Sufyan ya ce Sanatan na Sokoto ya bada gudumuwa sosai, kuma cikakken ‘dan siyasa ne wanda ya san kan aiki.

Har yanzu tsohon Gwamnan bai fito da niyyarsa ba, matashin ya ce ta haka ne za ayi wa ‘Yan Arewa maso yamma sakayya kuri’un da suka ba APC a 2023.

'Yan adawa su na tuggu

Wani rahoto da muka fitar ya nuna idan APC tayi wasa, 'ya 'yan PDP, LP, NNPP, da SDP za su hada-kansu, su fito da 'dan takarar shugaban majaliar tarayya.

Kara karanta wannan

Yadda Yahaya Bello Ya Kinkimo ‘Danuwansa, Ya ba Shi Takarar Gwamnan Kogi – Sanatan APC

Ganin su na da ‘yan majalisa har 182, ‘Yan adawa sun ce rinjaye yana hannunsu a 2023. A maimakon su bi bayan APC, jam’iyyun za fito da ‘dan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng