Yadda Yahaya Bello Ya Kinkimo ‘Danuwansa, Ya ba Shi Takarar Gwamnan Kogi – Sanatan APC
- Wasu daga cikin wadanda su ka so samun takarar Gwamna a Kogi sun yi fushi da Jam’iyyar APC
- Sanatan Yammacin Kogi a Majalisar Dattawa, ya fi daukar abin da zafi, ya caccaki Yahaya Bello
- Gwamnatin Bello ta maidawa Sanata Smart Adeyemi martani, ta kira shi da tsohon maci-amana
Kogi - Daya daga cikin wadanda suka yi fushi da zaben tsaida gwani na Gwamna a Kogi, Smart Adeyemi ya zargi Gwamna Yahaya Bello da karfa-karfa.
Punch ta ce Sanata Smart Adeyemi yana cikin wadanda ba su ji dadin abin da ya faru a zaben tsaida ‘dan takaran da jam’iyyar APC ta shirya a Kogi ba.
Da aka zanta da shi a tashar Channels a ranar Litinin, Sanatan da ya nemi tikiti ya rantse cewa APC ba tayi zabe wajen fito da ‘dan takara Gwamna ba.
A cewar Adeyemi, sakamakon bogi aka hada a Lokoja, aka aikawa uwar jam’iyya a Abuja.
Ododo 'danuwan Gwamna ne
"Shi wannan (Ododo) wanda ake cewa ya lashe zaben, kakansa daya da Gwamna Yahaya Bello.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babu wani zaben da aka yi, idan aka yi haka, za a zo lokacin da Gwamnan zai kakabawa mutanen jihar nan yaron cikinsa. Wannan ne mafi munin kama-karya.
- Smart Adeyemi
"Dama can maci amana ne" - Kogi
Da aka yi hira da Kwamishinan yada labarai da sadarwan a tashar Arise, Kingsley Fanwo ya musanya zargin ‘dan majalisar, ya ce APC tayi zabe na adalci.
Kingsley Fanwo ya maida martani ga kalaman Adeyemi wanda ya soki uban gidansa, shi kuma yake cewa Sanatan ya yi suna sosai wajen cin amana.
Kwamishinan ya yi wa ‘dan takaran gori da cewa ya yi takara a 2007, 2011 da 2015 amma duk bai ci zabe ba, sai da Yahaya Bello ya taimaka masa a 2019.
Fanwo ya ce tun farko an yi ta jan-kunnen Mai girma Gwamna, Adeyemi zai ci amanarsa.
...A dakatar da shi - Kungiyar 'Yan APC
Ana haka sai ga rahoto daga Daily Post cewa wata kungiya ta ‘yan APC su na bada shawarar a dakatar da Sanatan na yammacin jihar Kogi daga jam’iyya.
Shugaban kungiyar, Kwamred Kamaldeen Toyin, ya kira taron ‘yan jarida a garin Lokoja, a nan ya zargi Adeyemi da yin rana ga wanda ya yi masa inuwa.
Na hannun daman ya hakura
Edward Onoja wanda ake yi wa kallon 'yan gaban goshin bai samu tikitin APC ba, a baya an ji labarin yadda mataimakin Gwamnan ya janye takararsa.
Mutum 8 su ka janye takararsu bayan ganin alamar za a tsaida Usman-Ododo. A cikinsu har da shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati da Akanta Janar.
Asali: Legit.ng