INEC Ta Buƙaci Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Hukuntan Kwamishinan Zaben Adamawa

INEC Ta Buƙaci Sufetan Yan Sanda Na Kasa Ya Hukuntan Kwamishinan Zaben Adamawa

  • Hukumar zabe ta ƙasa ta bukaci Sufetan yan sanda ya gaggauta bincikar REC ɗin Aɗamawa kuma a gurfanar da shi
  • A taron da ta gudanar yau a Abuja, INEC ta cimma matsayar ɗaukar matakai uku kan abubuwan da suka taso daga zaben Adamawa
  • Ta kuma tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zata ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka kammala

Abuja - Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta cimma matsaya kan matakan da zata ɗauka biyo bayan matsalar da ta taso yayin tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa.

INEC ta amince zata rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban rundunar yan sanda na ƙasa, IGP Usman Baba, domin ya gudanar da bincike da gurfanar da dakataccen kwamishinan zaɓe (REC) na Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari.

Kara karanta wannan

Baki Ɗaya Kwamishinonin INEC Na Kasa Sun Shiga Taro Kan Zaben Adamawa, Bayanai Sun Fito

Mahmud Yakubu.
Shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: InecNigeria
Asali: Twitter

INEC ta cimma matsayar ɗaukar wannan matakin kan REC ɗin ne saboda ya ayyana Aishatu Ɗahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamna.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin Tuwita, INEC ta yanke ɗaukar wannan matakin ne a wurin taron da ta kira yau Talata domin tattauna batutuwan da suka taso daga zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A taronta na yau Talata 18 ga watan Afrilu, 2023, hukumar zaɓe ta tattauna batun da ya taso daga zaben gwamna a jihar Adamawa kuma ta cimma matsaya kamar haka:
"1. Zata rubuta takarda zuwa Sufetan yan sandan ƙasar nan domin gaggauta gudanar da bincike da kuma yuwuwar gurfanar da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari."
"2. Zata roki Sakataren gwamnatin tarayya ya ja hankalin mahukunta masu alhakin naɗe-naɗe game da wannan halayyar ta REC domin ɗaukar mataki na gaba."

Kara karanta wannan

Boye-Boye Ya Kare, Ranar Da INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Ta Bayyana

"3.Za'a ci gaba da tattara sakamako a kan lokaci wanda baturen zaɓe zai jagoranta kuma ya sanar idan ya ƙarƙare," INEC ta rubuta a shafinta na Tuwita.

INEC fa shiga ganawar sirri a Abuja

A ɗazu, mun kawo muku labarin cewa Kwamishinonin Hukumar Zabe INEC Sun Shiga Taron Gaggawa a Abuja

Taron dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan hukumar ta dakatar da kwamishinan zaben jihar Adamawa, Hudu Ari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel