Hadiza Bala Usman Ta Rubuta Littafin da Ya Tona Abin da Ya Jawo Amaechi Ya Kore ta a NPA
- Hadiza Bala Usman ta rubuta littafin da ya yi bayani a kan wa’adinta a Hukumar NPA ta kasa
- ‘Yar siyasar ta ce Ministan sufuri na lokacin, Rotimi Amaechi ya dauki karon tsana ya daura mata
- A karshe Amaechi ya ga bayan Bala Usman, duk da an yi ta kokarin a lallabi Ministan tarayyar
Abuja - Tsohuwar shugabar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman ta rubuta littafin da ya yi bayani a kan sabanin da aka samu da ita a lokacin ta na ofis.
Premium Times ta ce Hadiza Bala Usman ta zargi Mai gidanta, Rotimi Amaechi da korarta daga ofis saboda ta ki taimaka masa da wasu alfarma.
Bala Usman ta kira littafin da “Stepping on Toes: My Odyssey at the Nigerian Ports Authority”, ma’ana takalmin karfe, labari na a hukumar NPA.
Littafin na Bala Usman ya zargi Ministan sufuri na lokacin watau Rotimi Amaechi da jin haushinta saboda kurum ba tayi masa abin yadda yake so.
Gwamnoni sun nemi su tsoma baki
‘Yar siyasar ta ce Amaechi ya nuna wannan a lokacin da kungiyoyi a jagororin APC suka nemi su tsoma baki a lokacin da aka dakatar da ita daga aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar Atiku Bagudu ta kungiyar Gwamnonin APC ta zauna da Ministan kan maganar, ya dage dole sai an bincike ta domin an boye wasu kudi.
"Da Gwamnonin su ka matsa masa, sai ya fada masa yanzu abin ya fi karfin teburinsa, sai su tuntubi shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Ya fadawa wani da ya nemi ya sa baki na cika son-kai, babu alherin da na yi masa a NPA, ban taba ba shi kyautar murnar ranar haihuwarsa ba.
- Littafin Hadiza Bala Usman
A cewar Bala Usman, Ministan (na lokacin) ya hakikance a kan dole sai ta bar ofis, ya bukaci tayi murabus ko dai ta kalubalanci matakin a gaban kotu.
"Ba zan yi ritaya ko in je kotu ba" - Hadiza Bala Usman
Daily Nigerian ta ce tsohuwar shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin Kaduna ba ta karbi shawarar ba, musamman ganin an kafa kwamitin da zai bincike ta.
Ganin ta ki yarda da hakan, ta na ikirarin kwamitin zai gano ba tayi laifi ba, sai Amaechi ya yi alwashin ba za a kammala binciken ba har zuwa 2022.
Burinsa a lokacin shi ne a kai lokacin da aka buga gangar siyasa, take cewa sai a manta da maganar.
Kwamitoci sun zuke Biliyoyi
Tsakanin 2015 zuwa yanzu, Shugaban Kasa ya rantsar da kwamitocin gwamnati kimanin 40 an ji labari Kwamitocin nan sun ci wa Najeriya N20bn.
Boss Gida Mustapha da Babachir David Lawal ne suka rike ofishin SGF a shekaru 8 da suka wuce. Wasu su na ganin kwamitocin ba su da wani amfani.
Asali: Legit.ng