Ana Shirin Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, Wata Jam’iyya Ta Kai Tinubu Kotu

Ana Shirin Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, Wata Jam’iyya Ta Kai Tinubu Kotu

  • All Peoples Movement ta na ganin bai dace a rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a Mayun 2023 ba
  • Jam’iyyar adawar ta ce Bola Tinubu ya saba doka a wajen gabatar da sunan abokin takararsa
  • Lauyan APM ya zargi Kashim Shettima da shiga takara biyu a zaben 2023, ya ce yin hakan laifi ne

Abuja - Jam’iyyar nan ta APM ta ce nasarar da Asiwaju Bola Tinubu ta na tangal-tangal ta fuskar shari’a saboda yadda ya dauko Kashim Shettima.

Premium Times ta fitar da rahoto a daren Litinin cewa APM ta shigar da kara gaban kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa da ke garin Abuja.

Jam’iyyar hamayyar ta na ikirarin ‘dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 watau Bola Tinubu bai bi ka’ida a wajen bada sunan abokin gaminsa ba.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki a Gaban NNPP a Kano, APC Za Ta Karbe Nasarar Abba a Zaben Gwamnan 2023

A dalilin haka, APM ta roki kotun ta ayyana Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a karkashin PDP, a matsayin shugaban kasar Najeriya mai jiran gado.

A rantsar da Atiku - APM

Lauyoyin jam’iyyar su na so ayi fatali da kuri’u miliyan 8.8 da APC ta samu a zaben da aka yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce jam’iyyar APM wanda ‘dan takararta a 2023, Chichi Ojei ya tashi da kuri’u 25,961 ta ce APC ba ta goyi bayan takarar Bola Tinubu ba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya hadu da Atiku Abubakar Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Batun Ibrahim Masari da Shettima

A lokacin da ya tashi maida takardar shiga takara a ofishin INEC a 2022, Tinubu ya bada sunan wani Ibrahim Masari ne, daga baya aka canza shi.

Jaridar ta ce sai bayan an gabatar da Masari ne sannan tsohon Gwamnan na Legas ya dauko Sanata Kashim Shettima, INEC ta na shirin rufe kofa.

Kara karanta wannan

Kotun ƙoli tayi Fatali da Ƙarar Nwajiuba dake Fatan Ta Nuna Rashin Cancantar Takarar Tinubu da Atiku

A nan ne APM ta samu mafaka, ta na cewa jam’iyyar APC ta bada sunan Shettima sau biyu domin ya cike fam din neman Sanatan Borno ta tsakiya.

APM ta fadawa kotu cewa zababben mataimakin shugaban kasar ya shiga takara biyu a lokaci guda, ta kuma gabatar da hujja da za ta gaskata haka.

Masu shigar da karar sun kara da cewa janyewar da Masari ya yi a zaben bayan an kawo sunan tsohon Gwamnan na Borno, ya ruguza takarar Tinubu.

OM Atoyebi SAN ya kafa hujja da sashe na 131 (C) da na 142 su na masu cewa a lokacin da APC ta cire sunan Masari, wa’adin da INEC ta bada ya kure.

Gwamna Abia ya koka

An ji labari Dr Okezie Ikpeazu ya ce tazarar nasara a zaben Sanatan da ya shiga ba ta kai 30, 000 ba, ya so a ce INEC tayi hukunci cewa zaben bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Soke Bikin Cika Shekara 71, Ya Komawa Allah Gadan-Gadan a Bana

Amma duk da haka, Gwamnan mai barin gado da aka dankara da kasa ya bada shawarar a hakura da kai kara kotu, a bar Alex Otti ya ji dadin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng