“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Wani Mutum Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi
- Wani magoyin bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya haddasa yar dirama a jirgin saman Ibom
- Ana tsaka da shirin tashi daga Abuja zuwa Lagas sai mutumin ya fasa ihu cewa ba Bola Tinubu bane ya ci zabe kuma ba za a rantsar da shi ba
- Ya kawo tsaico ka tashin jirgin na kimanin awa daya inda a karshe aka kama mutumin aka fita da shi don ya zama barazana ga tashin jirgin
Abuja - An gano wani dan Najeriya a bidiyo yana zanga-zanga a kan batun rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, kamar yadda aka tsara a ranar 29 ga watan Mayu.
An tattaro cewa mutumin cikin bidiyon ya kawo tsaico wajen tashin jirgin sama na kamfanin Ibom daga Abuja zuwa Lagas har na fiye da awa daya, yana mai ikirarin cewa ba Bola Tinubu bane ya ci zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Yadda abun ya faru
An jiyo sauran mutanen da ke cikin jirgin suna cewa shi din barazana ne ga tashin jirgin sama kuma akwai bukatar a fitar da shi daga cikin jirgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu kuma sun bukace shi da ya je kotu ya kalubalanci sakamakon zaben idan har da gaske ba Tinubu bane aihanin wanda ya lashe zaben.
A ranar Laraba, 1 ga watan Maris ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Taheereffizie ya ce:
"Wawa yana ihun Obidienta. Za a rantsar da Asiwaju Insha Allah."
@detalentedhero ya ce:
"Ya kamata DSS su kwamushe shi. Lokacin da APC ta yo hayan limaman coci na san akwai karin abubuwa da za su biyo baya."
@Faceindahse ya yi martani:
"Dirama dirama dirama APC ta siya masa tikiti don ya zo ya nishadantar da fasinjoji."
Matashi ya yi farin ciki bayan butum-butumi ya gabatar masa da abinci a gidan abinci
A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya yi matukar farin ciki bayan ya isa wani gidan cin abinci idan butum-butumi ne ya gabatar masa da odan sa.
Asali: Legit.ng