Ko "Diris" Ba Zan Saka Hannu Na a Cikin Gwamantin Kano Mai Zuwa Ba - Kwankwaso

Ko "Diris" Ba Zan Saka Hannu Na a Cikin Gwamantin Kano Mai Zuwa Ba - Kwankwaso

  • Zarge zarge yayi yawa cewar, tunda Abba Kabir Yusuf yaci zaɓen gwamnan jihar Kano, Kwankwaso ne zai juya gwamnatin
  • Kwankwaso ya fito yayi martani mai ratsa jiki, bayan yace masu faɗin haka nayi ne kawai don son rai
  • Jagoran masu saka jari hular Kwankwasiyya na Kano, bazai juya gwamnatin Abba ba, amma zai bada shawara in aka buƙaci haka

Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, kuma ɗan takarar jam'iyyar na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Dr Rabi'u Musa Kwankwaso yayi wani batu dake nuna martani ga masu cewa zai juya gwamnatin Kano mai zuwa.

Jagoran siyasar na jihar Kano, yace ba zai taɓa zama wanda zai hana ruwa gudu a gwamnatin dake shirin zuwa ta Abba Kabir Yusif ba.

Kwankwaso ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma sayar da kadarorin jihar Kano da suka haɗa da makabartu, makarantu, dadai sauransu.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Buhari Na Musgunawa Ni, El-Rufai da Ganduje Saboda Mun Kalubalanci Canja Fasalin Kudi" - Matawalle

Kwankwaso
Ko "Diris" Ba Zan Saka Hannu Na a Cikin Gwamantin Kano Mai Zuwa Ba - Kwankwaso
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaida haka ne a wani shiri da sashin Hausa na BBC suka shirya ranar juma'ar nan.

Tsohon ministan tsaron da ya mulki Kano sau biyu dake ya furta cewar, gwamantin NNPP wacce zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusif zai jagoranta, zata maida ƙwarya gurbin ta wajen dawo da duk abinda aka lalata zuwa tsari.

Kwankwaso ya kuma maida martani akan muryar mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna akan taya murna da yayiwa Abba Kabiru Yusif murnar na cin zaɓe, tare da ɗaukan ƙaddara ta faɗuwa.

Inda yace:

“Haka ake ɓukata a ga mutum yayi. Ya nuna hali mai kyau wanda bana ko a mutu ko ayi rai ba". Inji Kwankwaso.

Daga karshe, shugaban tafiyar jar hular na kwankwasiyya, ya kuma tabbatar da cewar, idan har sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusif ta soma aiki, bazai ruwa yayi tsaki wajen ganin sai abinda yake so za'ai ba.

Kara karanta wannan

Zabaɓben Gwamnan APC a Jihar Sakkwato Ya Roki Tambuwal, PDP da Wasu Mutane Abu 1

Inda yace, a matsayin sa na babba kuma ɗan jihar, zai iya ɗaura shi akan hanya mai kyau, ko bashi shawara yayin daya buƙaci yin hakan, rahoton jaridar Vanguard.

Gwamnan jihar Jigawa Ya Karɓi Baƙuncin Likitoci Sittin da Jigawa ta Tura China Koyon Likitanci

Aƙalla yan Jigawa 60 ne suka samu tarba ta musamman daga wajen Gwamna Badaru na jihar Jigawa.

Likitocin da suka dawo gida cikin shekaru 6 sun dawo cike da farin ciki da ƙwarewa kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel