"Gwamnatin Tarayya Ta Hukunta Mu Nida El-Rufai da Ganduje Saboda Mun Kalubalanci Canja Fasalin" - Matawalle

"Gwamnatin Tarayya Ta Hukunta Mu Nida El-Rufai da Ganduje Saboda Mun Kalubalanci Canja Fasalin" - Matawalle

  • Gwamnan jihar Kano, Ganduje da Matawalle na Zamfara da El-Rufai na Kaduna sun maka FG a kotu akan dokar sauya fasalin kuɗi
  • Shari'ar da suka shigar haɗe da wasu gwamnoni, sunyi nasara akan gwamnatin tarayya tun kafin zaɓe
  • Gwamna Matawalle yace ya fadi zaɓe ne saboda wannan ƙara, inda Uba Sani yasha daƙyar yayin da Gawunan Ganduje yasha kayi shima

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwar sa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Najeriya CBN yayi.

Gwamnan ya zargi cewar, wasu fulogai a cikin gwamnatin tarayya da yin yaƙi dashi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba.

Idan za'a iya tunawa dai, Matawalle yayi takara ne a jam'iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ta kayar dashi.

Kara karanta wannan

"Ina Da Ikon Naɗa Duk Wanda Na So Har 29 Ga Mayu" Gwamnan PDP Ya Maida Martani

Matawalle
Canja Fasalin Kuɗi: Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Hukunta Mu Nida El-Rufai da Ganduje - Matawalle Hoto: Legit.ng
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da ƙari, gwamna Nasir El Rufai na Kaduna, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sun kai ƙarar Gwamnatin Tarayya zuwa Kotun ƙoli.

Abisa yunƙurin canja fasalin kuɗi tare da taƙaita anfani dasu wanda CBN ke aiwatar wa.

Matawalle yace:

"Ance tunda munje Kotu akan canja fasalin kuɗi na Naira. To dani, da Ganduje da El-Rufai duk sai an hukunta mu."

To amma daga wani tsagin, za'a iya tunawa Uba Sani na jam'iyyar APC da El-Rufai yake marawa baya yasha daƙyar.

Yayin da ɗan takarar da Ganduje ke marawa baya, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yasha kayi a hannun ɗan takarar jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.

Matawalle yace, yadda aka cika akwati-akwati da sojoji, hakan na nufin zargin sa daidai ne, domin yace anyi haka ne don a musgunawa masu kaɗa kuri'a shi kuma ya faɗi.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

A rahoton jaridar Vanguard anjiyo Matawalle yana karkarewa da:

"Kwana uku zuwa zaɓen gwamnan, sai aka turo sojoji mota 300, zuwa Zamfara.
"Adadin sojojin, da ace zasu turo mana su a yaƙi rashin tsaro, da abin ya bada citta. Amma sai suka turo mana su lokacin zaɓe,"

APC Tana Shirin Karɓe Nasara Daga Hannun Abba Gida-Gida na NNPP

A wani labari mai alaƙa da siyasa, jaridar legit.ng ta ruwaito cewar, da alama tsuguni bata ƙare ba ga jam'iyya NNPP mai shirin amsar mulki a jihar Kano.

Jam'iyyar APC ta jihar Kano, tace tana nan akan bakanta na tafiya kotu duk da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya amshi faɗuwa da kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Online view pixel