Gwamna Badaru Na Jigawa Ya Tarbi Likitoci 60 Da Jihar Ta Tura China Karatu

Gwamna Badaru Na Jigawa Ya Tarbi Likitoci 60 Da Jihar Ta Tura China Karatu

  • Dalibai yan asalin jihar Jigawa da gwamnatin jihar ta tura kasar Sin don yin karatun likitanci sun dawo gida a karo na farko cikin shekaru shida
  • Sun gana da gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar don masa godiya kan damar da gwamnatin jihar ta basu na amfana da gurbin karatun, inda 32 cikinsu sun kammala karatu
  • Salisu Mu'azu, sakataren Ma'aikatar Lafiya na jihar Jigawa ya ce an tura likitocin 32 zuwa Asibitin Kwararru na Rashin Shekoni da ke Dutse don koyon makamashin aiki kafin a tura su asibitocin jihohi

Jihar Jigawa - Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, a ranar Alhamis, ya tarbi daliban likantanci da gwamnatin da dauki nauyin karatunsu a kasar China.

Gwamna Badaru ya gana da daliban ne a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar ta Jigawa.

Kara karanta wannan

Kuna ruwa: Abba Gida-Gida ya tura sako ga duk wanda ya sayi filin gwamnati a jihar Kano

Gwamnan ya bada umurnin a bada aiki nan take ga 32 cikin daliban 60 da suka kammala karatunsu, Premium Times ta rahoto.

Likitoci da Badaru
Gwamna Badaru na Jihar Jigawa tare da likitoci da jihar ta tura China karatu. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Badaru ya umurci a bawa sabbin likitocin aiki a jihar Jigawa

Mista Badaru ya bada wannan umurnin ne a yayin da wasu cikin daliban suka ziyarce shi don masa godiya bisa gudunmawa da damar da gwamnatinsa ta ba su a 2016.

Bayan ziyarar, sakataren dindindin na Ma'aikatar Lafiya na jihar, Salisu Mu'azu, ya fada wa manema labarai cewa 28 cikin daliban har yanzu ana tabbatarwa da satifiket dinsu a Najeriya.

Mista Mu'azu ya ce:

"Gwamnatin jihar a shekarar 2016 ta zabi dalibai 60 masu kwazo daga mazabu daban-daban a jihar kuma sun dawo gida bayan shekaru shida na karatun likitanci.
"A halin yanzu mun tarbi 32 cikin dalibai 60 wadanda suka kammala karatunsu na likitanci kuma sun ci jarrabawarsu na likitanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jihar Borno Zata Ginawa Yan Gudun Hijira Gidaje 20,000 Kauyuka 3

"Da hakan, sun zama cikakkun likitoci masu rajista da za su iya aiki a Najeriya. An tura likitocin 32 Asibitin Kwararru Na Rasheed Shekoni a Dutse don koyon makamashin aiki na shekara daya kafin a tura su asibitoci daban-daban a jihar."

Manufar tura daliban zuwa China su yi karatun likitanci - Mu'azu

A cewarsa, manufar ita ce samar da ma'aikatan da za su gudanar da sabbin asibitoci da cibiyoyin lafiya kanana da manya da aka gina a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel