Zaɓabben Gwamnan Jigawa, Namadi, Ya Bayyana Gagarumin Aiki Guda Da Zai Yi Cikin Shekaru Huɗu

Zaɓabben Gwamnan Jigawa, Namadi, Ya Bayyana Gagarumin Aiki Guda Da Zai Yi Cikin Shekaru Huɗu

  • Zababben gwamnan jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa za ta rage talauci da kashi 50 zuwa 60 cikin shekaru hudu
  • Namadi, a cikin wata hira da aka yi da shi ya ce gwamnatin ta fara karfafawa masu kananan sana'a da matsakaita, manoma da masu noman rani gwiwa da wasu tsare-tsaren
  • Jihar Jigawa tana da kimanin mutane miliyan 5.76 da ke rayuwa cikin talauci a jihar

Jihar Jigawa - Umar Namadi, zababben gwamnan jihar Jigawa ya yi alkawarin rage talauci a jihar zuwa akalla kashi 50 zuwa 60 cikin 100 a zangon mulkin sa na farko, rahoton Daily Trust.

A cewar Hukumar Kiddiga na Kasa, NBS, a rahoton ta na baya-bayan nan akwai mutum miliyan 5.76 da ke fama da talauci a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Sarkin Saudiyya Ya Tuna da Mutanen Jihar Kano Yayin da Aka Soma Azumin Ramadan

Umar Namadi
Zababben gwamnan Jigawa ya yi alkawarin rage talauci da kashe 50 cikin shekaru hudu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Rahoton UNICEF shima ya ce jihar na da yara da ke rayuwa cikin talauci da suka kai kashi 73.9 cikin 100, hakan ya sa jihar ke kan gaba a bangaren talauci idan aka kwatanta da sauran sassan kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne cikin rahoton hukumar na 2021 Multiple Indicator Cluster Survey (MICS 6) da aka yi a kananan hukumomi 27 na jihar.

Hanyoyin da zan bi don rage talauci a Jigawa, Namadi

Da ya ke amsa tambayoyi a hirar da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Namadi ya ce yana da shirin rage talauci a jihar sosai.

Ya ce:

"Muna da niyyar karfafa gwiwa da tallafawa kanana da matsakaicin yan kasuwa, za mu yi kokarin wayar da kansu tare da ba su tallafin kudi. Da hakan tabbas za mu rage talauci.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutum 24 Sun Mutu Yayin Da Wata Babban Mota Da Ta Tashi Daga Zaria Zuwa Legas Ta Yi Haɗari

"Bugu da kari, mun san cewa Jigawa jihar manoma ne. Mun yi kokari sosai a bangaren noma wanda ya taimakawa wurin habbaka tattalin arzikin jihar.
"Yanzu za mu fadada kan hakan, za mu fadada noman rani mu kuma karfafa gwiwar masu bincike da cigaba. Za mu hada kai da abokan aiki na gida da kasashen waje don su saka jari a noma."

Ya cigaba da cewa:

"Idan an yi hakan, muna ganin za a samar da aiki sosai, samar da tsaro na abinci da habbaka kudin shiga a jihar.
"Tabbas da wannan tsare-tsaren da muke da su da niyyar mu na habbaka su, muna ganin zuwa karshen zangon mu na farko za mu iya rage talauci a Jigawa da kashi 50 ko 60."

AbdulSamad Ya Zama Na Hudu A Jerin Masu Arziki A Afirka

Hamshakin dan kasuwan Kano, Alhaji AbdulSamad Rabiu ya zama mutum na 4 cikin mafi yawan kudi a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Hakan na zuwa ne bayan ya doke attajirin Masar, Nassef Sawarus a cikin yan watanni hakan yasa ya zama na biyu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel