Umar Iliya Damagum: Muhimman Bayanai 10 a Game da Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP
Abuja - Ba sabon labari ba ne cewa majalisar gudanarwa ta PDP ta nada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban jam’iyya na riko.
Daily Trust ta fitar da rahoto game da abin da aka sani a kan rayuwa da siyasar Ambasada Umar Iliya Damagum wanda zai rike jam’iyyar PDP.
Wanene shugaban rikon kwaryar:
1. A ranar 10 ga watan Agustan 1963 aka haifi Umar Iliya Damagum, hakan yana nufin a shekarar nan zai cika shekaru 60 a Duniya.
2. An haifi Umar Ililya Damagum ne a garin Damagum wanda yanzu haka yana karkashin karamar hukumar Fune a jihar Yobe.
3. ‘Dan siyasar ya yi firamare akauyensa daga 1971 zuwa 1977, daga nan ya tafi Maiduguri a jihar Borno domin yin karatun sakandare.
4. Bayan gama sakandare a 1982, Damagum ya samu fara karatun sharar fage a jami’ar UNIMAID, ya yi karantu tsakanin 1982-83.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
5. A Jami’ar Maiduguri ne Umar Ililya Damagum ya samu digirin B. A a fannin koyar da karatu, ya karanci ilmin koyar da fasaha.
6. A shekarar 2003, Damagum ya sake komawa jami’ar da ke kusa da shi domin yin digirgir, a nan ya samu digirn M. BA na ilmin kasuwanci.
7. A lokacin Gwamnatin Olusegun Obasanjo, ‘dan siyasar ya zama Jakadan Najeriya zuwa Romaniya, ya rike kujerar daga 2004 zuwa 2007.
8. Damagum ya nemi zama Gwamnan jihar Yobe a karkashin PDP a 2019, amma Mai Mala Buni ya doke shi, ‘dan takaran bai je kotu ba.
9. Bayan ya sha kashi a zaben sabon Gwamna, Ambasada Damagum ya fito takarar mataimakin shugaban PDP na kasa, kuma ya yi nasara.
10. Kafin ya zama shugaban jam’iyya na rikon kwarya, Damagum shi ne babba a cikin mataimakan Iyorchi Ayu a NWC, yana wakiltar Arewa.
"Ko me zai faru sai da ya faru" – Wike
A ranar Litinin aka rahoto Nyesom Wike yana cewa babu dalilin da Iyorchia Ayu zai cigaba da zama Shugaban PDP domin bai amfanar da ita ba.
A zaben shugaban kasa; Gwamna Nyesom Wike ya ce PDP ta rasa rumfa, mazaba, karamar hukuma da jihar da Sanata Ayu yake tutiya da su.
Asali: Legit.ng