Zababben Gwamnan Katsina Ya Fadi Silar Fadin Tinubu a Jihar Shugaban Kasa
- Dikko Umaru-Radda ya na zargin an yi amfani da addini da kabilaci a zaben sabon shugaban kasa
- Zababben Gwamnan na jihar Katsina ya ce jama’a ba su damu sosai da wanda zai mulki Najeriya ba
- Kuri’un da aka kada bayan ‘yan makonni sun nuna mutane sun fi maida hankali a zaben Gwamnoni
Abuja - A wata hira da aka yi da shi, Dikko Umaru-Radda ya yi bayanin siyasar 2023, takararsa da yadda jam’iyyar APC ta rasa jihar Katsina a babban zaben shugaban kasa.
Dikko Umaru-Radda wanda shi ne zababben Gwamnan jihar Katsina ya ce bambancin addini da kabilanci ya yi tasiri wajen mutane a zaben shugaban kasa.
‘Dan siyasar ya shaidawa Daily Trust cewa mutane sun fi damuwa da zaben Gwamnan jiha da ‘yan majalisun dokoki a kan wanda zai zama shugaban kasa.
Ba za a iya cire kabilanci da ra’ayin addini musamman a asalin jihohin Arewa ba, gaskiyar abin da ya faru a zaben shugaban kasa kenan.
Ina ganin wannan ne ya yi tasiri aka samu wannan ratar kuri’u a zaben shugaban kasa a Katsina.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka zo zaben Gwamnoni, mutane sun fi maida hankali. Jama’a su na so su zabi Gwamnansu da ‘yan majalisar dokokin jihohinsu.
Manya ne su ka fi maida hankali game da zaben shugaban kasa domin su ne ke iya shiga Abuja, amma ‘yan karkara Gwamna su ka sani.
- Dikko Umaru-Radda
Dikko Radda: An daina duba Jam'iyya
A tattaunawar da ya yi da jaridar a Abuja, Dr. Dikko Radda ya ce wannan karo mutane ba su duba jam’iyya ba, cancanta da nagarta aka yi la’akari da su a 2023.
Zababben gwamnan ya ce yana da kalubale a gaban shi domin Katsinawa sun gamsu da shi.
Da zarar Dikko Radda ya zama Gwamna, abin da gwamnatinsa za ta fara maida hankali a kai su ne inganta tsaro da tattalin arziki da gyaran aikin gwamnati.
Tsohon shugaban na SMEDAN ya yi alkawari zai farfado da harkar kiwon lafiya da ilmi, sannan ya kafa hukuma ta musamman domin inganta rayuwar jama’a.
Birtaniya ta na sa ido
An samu labari cewa Birtaniya ta dauki mataki mai tsauri kan wasu 'Yan siyasa a dalilin bakin kamfe da suka yi a zaben 2023, wanda ke iya jawo rigingimu.
Kalaman da wadannan 'yan siyasa su ka rika yi, su na da hadari ga damukaradiyyar kasar nan, Jakadan Ingila ya ce za a hana biza ga masu wannan aika-aika.
Asali: Legit.ng