INEC Tayi Watsi da Kiraye-Kiraye, Ta Tsaida Ranar Rabawa Zababbun Gwamnoni Satifiket

INEC Tayi Watsi da Kiraye-Kiraye, Ta Tsaida Ranar Rabawa Zababbun Gwamnoni Satifiket

  • INEC ta zabi jerin ranakun da za ayi rabon satifiket ga ‘yan takaran da suka lashe zabukan Maris
  • Hukumar gudanar da zaben za ta bada shaidar nasara ga zababbun Gwamnoni da mataimakansu
  • ‘Yan takaran da suka yi nasara a zaben Majalisar dokoki za su samu satifiket a jihohinsu

Abuja - Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta ce za ta raba takardun shaidar nasara ga duka wadanda suka lashe zaben Gwamnoni.

A wata sanarwa da ta fitar a daren Lahadi, INEC ta ce za a mika satifiket ga zababbun gwamnoni da wadanda suka lashe zaben majalisar dokoki.

Za a fara wannan aiki ne daga ranar 29 ga watan Maris har zuwa ranar 31 ga watan mai ci a 2023.

Legit.ng Hausa ta fahimci wannan bayani ya fito ne a sanarwar da Festus Okoye ya fitar a matsayinsa na Kwamishinan yada labarai na INEC.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Festus Okoye ya fitar da jawabi

The Cable ta rahoto Festus Okoye yana cewa za a raba satifiket din ga wadanda suka yi nasara ne a ofisohin hukumar INEC da ake da su a Jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sashe na 72 (1) ya wajabtawa hukumar kasar bada takardar shaida ga ‘yan takaran da suka yi nasara, za ayi hakan ne kafin a zarce kwanaki 14.

INEC.
Jawabin INEC Hoto: @inecnigeria
Asali: UGC

Nasara ta tabbata a zaben 2023

A dalilin haka, Okoye ya ce daga ranar Laraba zuwa Juma’a mai zuwa, zababbun Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha za su karbi takardar nasararsu.

Zuwa lokacin za a sanar da masu jiran gadon game da lokacin da za su karbi satifiket dinsu, bayani zai fito ne daga bakin Kwamishinonin zaben jihohi.

Baya ga gwamnoni da ‘yan majalisun da za su shiga ofis nan da karshen Mayu, za a bada satifiket ga wadanda za su zama mataimakan Gwamnoni.

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisa Ya Sha da Kyar, An Kusa Kashe Shi, An Kona Motarsa Kurmus

A jihohi 28 hukumar INEC ta shirya zaben Gwamnoni a 2023 yayin da aka yi zaben ‘yan majalisar dokoki a kowace jiha da ake da ita a fadin kasar nan.

A halin yanzu akwai masu kiran a sake duba zabukan Gwamnoni da aka yi a Kano, Ogun, Adamawa, da alama dai hukumar ba ta da niyyar yin hakan.

Allura za ta tono garma?

A wani rahoto da aka fitar a ranar Asabar, an ji Sanata Uba Sani yana zargin cewa kuri'un PDP a zaben Gwamnan jihar Kaduna sun wuce hankali.

Uba Sani wanda ya lashe zaben Gwamna a Kaduna zai je kotu kuma ya musanya cewa APC tayi magudi, ya ce Ubangiji SWT ne mai bada mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng