INEC Ta Yi Mun Daidai da Ta Ayyana Zaben Adamawa da Bai Kammalu Ba, Binani

INEC Ta Yi Mun Daidai da Ta Ayyana Zaben Adamawa da Bai Kammalu Ba, Binani

  • Sanata Aishatu Binani, mai neman zama gwamnan Adamawa a inuwar APC ta yi magana kan zaben da ya gabata
  • Binani ta ce ayyana zaben gwamnan Adamawa da wanda bai kammalu ba ya mata daidai, ta faɗi dalilai
  • Akwai tazarar kuri'u sama da 30,000 tsakanin Binani da Ahmadu Fintiri, gwamna mai ci a inuwar PDP

Adamawa - Yar takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta nuna goyon bayan ayyana zaben jihar da 'bai kammalu ba.

Idan baku manta ba, baturen zaben INEC, Farfesa Muhammadu Mele, na jami'ar Maiduguri, ya ayyana zaɓen gwamnan Adamawa da bai kammalu ba watau 'Inconclusive' sabida tazarar dake tsakani.

Aishatu Binani.
Yar takarar gwamna a inuwar APC, Sanata Aishatu Binani Hoto: Aishatu Binani
Asali: Twitter

A rahoton Premium Times, Gwamna mai ci na PDP, Ahmadu Fintiri, ya samu kuri'u 421,524 yayin da babbar mai kalubalantarsa ta AP,C, Aishatu Binani, ta samu kuri'u 390,275.

Kara karanta wannan

Uba Sani: ‘Dan Takaran Gwamnan Kaduna Zai Kai Jam’iyyar PDP Kotu Duk da Ya Ci Zabe

A wata hira kai tsaye a gidan Talabijin ɗin Channels cikin shirin Politics Today, Sanata Binani ta yi maraba da matakin INEC na cewa zaben bai kammalu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binani ta yi zargin cewa an samu rikici da take doka a kananan hukumomi 16 cikin 21 dake faɗin jihar Adamawa.

Ta ce:

"Matsayar dana ɗauka ita ce kwamishinan INEC na jiha ya yi daidai da ya ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba kuma dalilaina a fili su ke."
"Duk wanda ya bibiyi zaben gwamnan da aka gudanar a Adamawa ya san cike yake da tashin tashina, magudi da aringizon kuri'u da sauran abubuwan take doka."

A cewarta, tsallake na'urorin BVAS suka yi, shiyasa suka samu damar aringizon kuri'u da kuma yi wa malaman zaɓe barazana a wurare da dama.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Enugu Mai Cike da Ruɗani

"Alal misali, idan BVAS ta tantance mutane 10, zaka samu mutane sama da 30 sun jefa kuri'u. Wannan wani bangare ne na abinda aka aikata."

A mahangar Aishatu Binani, hanya ɗaya da REC ɗin Adamawa zai wanke kansa shi ne ta ayyana zaben a matsayin 'Inconclisive' kuma hakan ya yi.

Bayan ɗaukar Lokaci INEC ta faɗi sakamakon Abiya

A wani labarin kuma Bayan Kai Ruwa Rana, INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Abiya

Bayan kwanaki da gama zaɓe, baturean zaben INEC na jihar Abiya ya sanar da wanda ya samu nasarar zama sabon gwamna a jigar dake kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel