‘Yan Kwanaki Da Cin Zaben Majalisa, Shehi Ya Koma Gabatar da Tafsirin Azumi a Kano

‘Yan Kwanaki Da Cin Zaben Majalisa, Shehi Ya Koma Gabatar da Tafsirin Azumi a Kano

  • Malam Abdulhakeem Kamilu Ado ya gabatar da karatu a KUST yayin da aka shiga watan Ramadan
  • A watan nan Abdulhakeem Ado ya lashe zaben Majalisa, zai wakilci mutanen Wudil da Garko
  • Shehin ya saba yin karatu a masallacin Jami’ar, nasarar zabe ba ta canza komai a wannan karo ba

Kano - A makon da ya gabata ne Abdulhakeem Kamilu Ado ya yi nasarar zama zababben ‘dan majalisar wakilan tarayya a Najeriya.

Wani abin ban sha’awa shi ne jim kadan da faruwar hakan, sai ga Sheikh Abdulhakeem Kamilu Ado yana karatu a watan Ramadan.

Dama can wannan Bawan Allah, malamin musulunci ne, kamar yadda ya saba, ya bude majalisin karatu a masallacin da ke jami’ar Wudil.

Falalar watan Ramadan

Khalifa Usman Abdullahi ya daura hotuna da bidiyo a Facebook inda za a iya ji matashin malamin yana bayanin falalar azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Sarakunan Kano Da Gaya Sun Taya Zababben Gwamnan Kano Murna, Sun Bashi Shawara

Malamin ya kawo Hadisin Annabi SAW yana cewa mafi alherin mutane shi ne wanda kwanakinsa suka yi tsawo, sannan aiki ya yi kyawu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda muka samu labari a shafin Twitter, Abdulhakeem Kamilu Ado ya soma karatun tafsirin Al-Kur’ani na watan Ramadan a Kano.

Abdulhakeem Kamilu Ado
Abdulhakeem Kamilu Ado da Rabiu Kwankwaso Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Musulmai sun yaba

Hakan ya jawo musulmai su na ta yabon zababben ‘dan majalisar tarayyar na Wudil da Garko.

Wani da ya kira kan sa Shagon Gawuna a Twitter, Mai bada shawara ne ga Shugaban karamar Hukumar Ungogo a Kano, amma ya yabi shehin.

A cewarsa, Sheikh Abdulhakim Ado shi ne babban alherin da NNPP da Kano su ka samu, da yake magana a Twitter ya roki Allah ya tsare shi.

Sauran jama’a kuwa sai cewa su ke yi Ma Sha Allahu, an ga ‘dan majalisa mai jiran gado a dakin Allah, yana yi wa al’umma wa’azi a cikin azumi.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

Ba kasafai aka saba ganin ‘yan siyasa a irin wannan matsayi, Darektan cibiyar Al-Auza’i da ke nazari da binciken a kan Musulunci, ya fita zakkah.

Wanene Abdulhakeem Kamilu Ado?

A baya kun ji labari wannan malami mahaddacin Alqur'ani ne kuma makarancin Hadisin Mjanzon Allah (SAW) da fikihu, sannan ‘Dan Boko.

Zuwa yanzu, matashin mai shekara 30 yana koyarwa a jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila, yana karantar da addini a KUST da wasu majalisan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng