Abba Gida-Gida, Zulum da Sauran 'Yan takara 6 Masu Yawan Kuri'u a Zaben Gwamna
- New Nigeria Peoples Party, NNPP ta yi galaba a zaben Kano da kuri’un da sun zarce miliyan guda
- Akwai ‘Yan takaran All Progressive Congress da suka lashe zabe da ratar 300, 000 zuwa 400, 000
- Mun tattaro ‘yan takaran da suke da kuri’u masu yawa ko kuma akalla suka bada rata sosai a 2023
1. Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da ya yi takara a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP ne kurum wanda ya samu kuri’u fiye da miliyan guda a zaben Gwamna da aka yi.
Zababben Gwamnan na Kano ya yi galaba a kan Nasiru Yusuf Gawuna da kuri’u 1,019,602, jam’iyyar APC da ta zo ta biyu ta na da kuri’u 890,705.
2. Babajide Sanwo Olu
A zaben Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi galaba a jam’iyyar APC, yana da kuri’u 762,134, shi kuwa Gbadebo Rhodes-Vivour ya samu 312,329.
Ko da kuri’u 450, 000 ne ratar ‘yan takaran biyu, mutum 62,449 sun zabi jam’iyyar PDP a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
3. Umaru Dikko Radda
Dr. Umaru Dikko Radda ya zama zababben Gwamnan Katsina ne da kuri’u 859, 892 a jam’iyyar APC. Yakubu Lado Danmarke na PDP yana da 486, 620.
Wannan rata ta kuri’a 370, 000 ta ba APC damar yin shekaru 12 ta na kan mulki a jihar Katsina.
4. Babagana Umar Zulum
Farfesa Babagana Umara Zulum zai zarce a kan kujerar Gwamnan jihar Borno a sakamakon gagarumar nasarar da ya samu a kan Mohammed Jajari.
Mai girma Gwamnan yana da kuri’u 545,543 shi kuwa ‘dan takaran PDP ya kare da 82,147. Tsakaninsu akwai tazarar fiye da kuri’u 460, 000 a zaben.
5. Seyi Makinde
Gwamnan Seyi Makinde yana cikin wadana suka ba abokan hamayyarsu tazarar raba-ni-da-yaro a 2023. Kuri’un PDP sun kusa ribanya na APC.
Kuri’un Jam’iyyar PDP a takarar Gwamna sun kai 563,756 alhali ‘dan takaran da APC ta tsaida, Sanata Tai Folarin yana baya da kuri’u 260, 000 a zaben.
6. Umar Namadi
A zaben sabon Gwamnan jihar Jigawa, Jam’iyyar APC ta tabbata ta bada ratar kuri’u 256,685, kuma tayi nasara a kananan hukumomi 26 da ake da su.
Mustapha Sule Lamido da PDP ta tsaida ya yi nasara ne a Birnin Kudu kadai, ya samu 368, 726, Umar Namadi ya ci zabe da 618, 449, NNPP ta zo ta uku.
7. Bala Mohammed
INEC ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed a zaben Gwamnan Bauchi a sakamakon kuri’u 525,280 da jam’iyyar PDP ta tashi da su a ranar Asabar.
Sadique Abubakar da ya tsaya a jam’iyyar APC ya zo na biyu a zaben, yana a kuri’u 432,272.
8. Caleb Muftwang
Da kuri’un da ba su haura 43,899 ba jam’iyyar PDP ta lashe zaben Jihar Filato a 2023. Barista Caleb Muftwang ya doke ‘dan takaran APC mai mulki.
Gaba daya Caleb Muftwang yana da kuri’a 525, 299, Farfesa Nentawe Yiltwada ya samu 481 370.
'Yan biyu babu a 2023
A rahotonmu kun ji yadda Yakubu Dogara ya ji kunya a zaben Shugaban kasa a PDP, sannan ya kunyata a zaben Gwamnan Bauchi da ya tsallaka APC.
Darektan yakin zaben Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal da irinsu Sule Lamido su na kallo APC ta lallasa PDP a duka zabukan da aka yi.
Asali: Legit.ng