Obi Bai Da Gaskiya; Ni Na Gabatar Da Shi Ga Atiku a 2019, Wike

Obi Bai Da Gaskiya; Ni Na Gabatar Da Shi Ga Atiku a 2019, Wike

  • Gwamna Nyesom Wike ya ce shine ya zabi Peter Obi a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar gabannin zaben shugaban kasa na 2023
  • Wike ya fadi hakan ne yayin da yake watsi da rade-radin cewa ya yi adawa da takarar Peter Obi yayin zaben shugaban kasa na 2023 da aka kammala
  • A cewar gwamnan na Ribas, ya zama makiyin masu karya dokar mulki na PDP da dama saboda ya zabi Obi sama da sauran mutane a 2019

Rivers - Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya yi watsi da rade-radin cewa ya yi adawa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu.

Gwamnan ya kuma bayyana yadda ya zabi Obi don zama abokin takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP gabannin zaben shugaban kasa na 2019, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

Gwamna Nyesom Wike da Peter Obi
Obi Bai Da Gaskiya; Ni Na Gabatar Da Shi Ga Atiku a 2019, Wike Hoto: Nyesom Wike, Peter Obi
Asali: Twitter

Abun da yasa mutane ke caccakar Myesom Wike kan kayen Peter Obi

Obi ya yi takara da Atiku a zaben shugaban kasa na 2023 kuma shine ya zo na uku, bayan dan takarar na PDP, inda ya samu kuri'u 6,101,533, rahoton Thisday.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ne ya lashe zaben inda ya kayar da Atiku da Obi, amma ana ta rade-radin cewa Gwamna Wike ya yi adawa da takarar Peter Obi.

Da yake jawabi ga wasu zababbun yan jarida a Port Harcourt a ranar Laraba, 22 ga watan Maris, Wike ya ce shi bai bukaci mutane da su zabi wani takamaiman dan takara ba illa hadin kan Najeriya.

Ya ce:

"A 2019, ku tambayi Peter Obi. Ina daya daga cikin tawagar da suka zabe shi don zama dan takarar mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar. Da muka hadu a gidan Abubakar, ya ce ga sunayen, zan zabi Obi."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

Gwamnan ya ci gaba da cewa an ga laifinsa kan zabar Obi da ya yi, yana mai cewa akwai sauran jerin sunayen wasu mutanen, ciki harda Pius Ayium, Ike Ekweremadu da wasu da dama.

Yan takarar shugaban kasa 4 sun shiga kotu don kalubalantar nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, mun jin cewa hudu daga cikin yan takarar shugaban kasa 18 sun shigar da kara kotun zabe a hukumance don kalubalantar nasarar Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng