"G5 Ba Ta Yanke Shawarin Mara Wa Peter Obi Baya Ba" Gwamna Wike

"G5 Ba Ta Yanke Shawarin Mara Wa Peter Obi Baya Ba" Gwamna Wike

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ko kaɗan gwamnonin G-5 ba su zauna sun amince da goyon bayan Peter Obi ba
  • Duk da an gama zaben 2023, Gwamna Wike ya ce tun farko tawagar adalci a PDP ta cimma maatsayat tabbatar da mulki ya koma kudu
  • Ya ce gwamnonin Enugu da Benuwai sun yi sadaukarwa mai girma, haka gwamnan Oyo ya lashi takobin tabbatar da adalci

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi ƙarin haske cewa ba bu wani lokaci da gwamnonin G-5 suka amince su goyi bayan ɗan takarar LP, Peter Obi, a zaben da ya gabata.

Rahoton The Nation ya ce gwamna Wike kuma jagoran tawagar G-5 ya faɗi haka ne a wata hira da manema labarai kai tsaye ranar Laraba 22 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni 28, Ta Ɗauki Mataki Kan Jihohi 2

Gwamna Wike na jihar Ribas.
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Ya bayyana cewa abu ɗaya da tawagar gwamnonin ta cimma matsaya shi ne zasu yi aiki don tabbatar da shugaban ƙasa na gaba ya fito daga kudancin Najeriya.

A rahoton The Cable, Gwamna Wike ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu wani lokaci da mambobin tawagar adalci suka zauna kuma suka yanke cewa dole wannan mutumin zamu bi. Abu ɗaya da muka amince shi ne mulki ya koma kudu."
"Mun amince da cewa koma menene ya zama tilas shugaban kasa ya dawo kudu, manufar G-5 kawai a yi adalci da daidaito."

Wike ya ƙara da cewa wasu daga cikin gwamnonin G-5 kamar Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da Samuel Ortom na Benuwai sun yi sadaukarwa mai girma don tabbatar da mulki ya koma kudu.

Ya ce duk da gwamna Makinde na Oyo ya samu nasarar tazarce, da farko ya ce ba zai damu ba don ya sadaukar da kudirin tazarcensa a yaƙin tabbatar da adalci da daidaito a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kwadayin Mukami? Tsohon Gwamnan PDP Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Sa Na Marawa Tinubu Baya

INEC ta gama aikin bitar zaben gwamnoni

A wani labarin kuma INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamna a Jihohi 28 wanda ya gudana ranar Asabar

Hukumar zaben ta kuma bayyana cewa yau 22 ga watan Maris, zata ci gaba da tattara sakamakon zabe a jihohin Abiya da kuma Enugu.

INEC ta ce kamar yadda ta yi alƙawari a taronta na ranar Litinin, ta bi sakamakon zaben gwamna ɗaya bayan ɗaya na baki ɗaya jihohi 28.

Asali: Legit.ng

Online view pixel