Amurka ta Jero Inda aka yi Aika-Aika a Zaben 2023, Ta Fadi Matakin da Za a Dauka
- Gwamnatin Amurka ta na zargin akwai inda aka hana Bayin Allah kada kuri’arsu a zaben bana
- A zaben Gwamnonin da aka yi, Jakadancin Amurka ta ce an yi rikici a Jihohin Kano da su Legas
- Ana zargin an yi amfani da kabilanci tun kafin zabukan, kasar wajen ta ce za ta dauki mataki a kai
Abuja - Gwamnatin Amurka ta bukaci Najeriya ta dauki matakin hukunta duk wadanda aka samu da laifi wajen hana mutane kada kuri’a a jihohi.
A wani rahoto na ranar Talata da ya fito daga Premium Times, an ji kasar Amurka tana zargin an samu fitintinu da zare idanu a zabukan Gwamnoni.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin Jakadancin kasar Amurkan da ke Najeriya a birnin tarayya Abuja.
"Mu na kira ga hukumomin Najeriya su hukunta kuma su yi adalci ga daidaikun da aka samu sun bada umarni ko sun rika razana masu yin zabe
Ko kuma su ka hana a kada kuri’a a lokacin zaben Gwamnonin jihohi."
- Jakadancin Amrurka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi aika-aika a zaben Asabar
Ofishin Jakadancin kasar wajen ya ce jami’anta masu lura da zabe sun tabbatar da an samu abubuwan da ba su dace ba a wajen zaben da ya gabata.
Jawabin ya ce kasar ta damu sosai da irin aika-aikar da suka faru a Legas, Kano da wasu Jihohi.
Baya ga haka, Amurka ta fahimci an yi amfani da kalamai na kabilanci a lokacin zaben Gwamnan jihar Legas wanda Jam'iyya mai-ci ta samu tazarce.
Jaridar ta ce Ofishin Jakadancin ya yabi ‘yan siyasa, malaman addini, matasa, jagororin al’umma da duk ‘yan kasa da suka soki wannan mugun hali.
Za a dauki mataki
A dalilin haka, Amurka za ta dauki duk matakan da ya dace daga hana bada biza ga mutanen da take ganin su na da hannu wajen murde zabukan kasar nan.
Duk da haka, an yaba da aikin INEC, jawabin ya ce an samu gyare-gyaren kura-kuran da aka yi, a karshe aka ba wadanda suka fadi shawarar da su sheka kotu.
Daga Jihohi 11 zuwa 0
Rahoto ya zo cewa wannan karo a zaben Gwamnonin jihohi, Jam'iyyar LP ba tayi nasara a Filato, Nasarawa, Ebonyi, Delta, Kuros Ribas ko kuwa Legas ba
Akwai yiwuwar Jam’iyyar tayi nasara Enugu ko Abia. Peter Obi ya samu kuri'u miliyan 6 a zaben shugaban kasa, amma har yanzu LP ba ta da Gwamna
Asali: Legit.ng