2023: INEC Ta Fitar da Sakamakon Zaben Yan Majalisun Jihar Edo
- Bayan kwana uku da zabe, Hukumar INEC ta saki sakamakon zaben mambobin majalisar dokokin jihar Edo
- Sakamakon ya nuna PDP mai mulki ta samu 'yan majalisu 12, APC ta ci guda 8, yayin da Labour Party ta samu 1
- Hukumar zabe INEC ta ayyana sakamakon zabe na mazaɓu uku da ba su kammalu ba
Edo - A ranar Talata, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sakamakon zaben mambobin majalisar dokokin jihar Edo wanda ya gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris.
A sakamakon wanda ya fito kwanaki uku bayan kammala zaɓe, jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta lashe kujeru 12 cikin 24 da ta shiga takara, APC ta ci guda Takwas.
Labour Party (LP) ta samu kujera ɗaya yayin da INEC ta ayyana sauran guda uku da ba su kammalu ba (Inconclusive) kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Yanzu Yanzu: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Zanga-Zanga Ke Gudana a Ofishin INEC Kan Ayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Wata Jiha
Sakamakon ya nuna cewa PDP ba ta ci ko ɗaya daga cikin kujerun 'yan majalisar tarayya da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu ba amma ta ba da mamaki a zaben jiha.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Vanguard tace hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban sashin ilimantarwa da yaɗa labarai na INEC, Timidi Wariowei, ya fitar ranar Talata 21 ga watan Maris, 2023.
Jerin mazabun da PDP ta samu nasara
Sanarwan ta nuna cewa PDP ta samu nasara a mazabun Akoko-Edo I, Akoko-Edo II, Esan ta tsakiya, Esan ta arewa maso gabas II, Esan ta kudu maso gabas, da Igueben.
Sauran inda PDP ta ci su ne, Ikpoba-Okha, Orhionmwon II, Ovia ta arewa maso gabas I, Ovia ta arewa maso gabas II, Owan ta yamna, da kuma Uhunmwonde.
Jerin mazabun da APC da LP suka samu nasara
Jam'iyyar APC ta yi nasarar lashe kujerun majalisar dokokin Edo a mazaɓun Esan ta arewa maso gabas I, Esan ta yamna, Etsako ta tsakiya, Etsako ta gabas, Etsako ta yamma I, Etsako ta yamma II, Orhionmwon I, da kuma Owan ta gabas.
LP ta lashe kujerar dan majalisar jiha ɗaya tal mai wakiltar mazabar Oredo ta yamma. INEC ta ayyana zaɓen mazabar Oredo ta gabas, Egor, da kuma Ovia ta kudu maso yamma a matsayin ba su kammalu ba.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Aike Da Sunayen Mutum 7 da Yake Son Naɗa Wa a NDIC Ga Majalisar Dattawa
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta wasiƙar bukatar shugaban kasa wanda ya nemi majalisar da tantance mutanen.
Asali: Legit.ng