A Karon Farko a Shekara 24, PDP tayi Nasara a Zamfara, Gwamnan APC Ya Rasa Tazarce
- Gwamna Bello Matawalle ba zai zarce a kujerarsa ba, ‘Dan takaran PDP ya doke shi
- Hukumar INEC ta tabbatar da cewa Lawal Dare ne zababben Gwamna a Zamfara a 2023
- Duk da ta yi mulki a baya, amma wannan ne karon farko da PDP ta lashe zabe a jihar
Zamfara - Rahotanni sun tabbatar da cewa Lawal Dare ya doke Bello Matawalle a zaben Gwamnan jihar Zamfara da aka shirya.
Mai girma Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya rasa tazarce a hannun ‘dan takaran jam’iyyar adawa ta PDP, Lawal Dare.
Daily Trust ta ce Alhaji Lawal Dare ya samu kuri’u 377,726 a zaben da aka shirya, Bello Mohammed Matawalle yana da 311, 976.
Baturen zaben Gwamnan jihar Zamfara, Farfesa Kasimu Shehu ya sanar da Lawal Dare a matsayin wanda ya yi nasara a takarar.
Jam'iyyar PDP ta ba APC rata
An samu ratar kuri’u 65, 800 tsakanin jam’iyyar PDP mai adawa da kuma APC mai mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Legit.ng Hausa ta fahimci jam’iyyar APC tayi nasara ne a kananan hukumomin Bakura, Birnin Magaji, Mafara da Muradun.
PDP kuwa ta samu nasara a sauran kananan hukumomin Anka, Bukuyum, Bungudu, Gumi, Gusau, Kaura, Maru, sai Shinkafi.
Haka zalika ‘dan takaran PDP watau Lawal Dare ya doke Gwamna mai mulki a Tsafe da Zurmi.
PDP ta taba cin Zamfara?
Wannan ne karon farko da jam’iyyar PDP ta lashe zaben Gwamna a jihar Zamfara tun 1999, duk da tayi mulki sau biyu a jihar.
PDP aka ba nasara a zaben 2019 a dalilin sabawa dokar zabe da APC tayi. A wancan lokaci Jam’iyyar PDP ta zo na biyu ne.
Sannan Zamfara ta taba zama karkashin PDP a lokacin da Mahmuda Aliyu Shinkafi ya sauya-sheka, ya rasa tazarce a 2007.
Zaben jihar Kebbi
A zaben Gwamnan Kebbi, an ji labari jam’iyyar APC ta na da 388,258 sai PDP ta samu kuri’u 342,980, babu wanda ya yi nasara.
Dalili kuwa shi ne INEC ta ce a yayin da ake tattara sakamako, an soke adadin kuri’u 91, 829 daga kananan hukumomi har 20
Asali: Legit.ng