Jam’iyyar NNPP ta Tona Shirin Ganduje, IGP Ya Aiko da Jirgi da Motoci Zuwa Kano

Jam’iyyar NNPP ta Tona Shirin Ganduje, IGP Ya Aiko da Jirgi da Motoci Zuwa Kano

  • Babbar jam’iyyar hamayya ta NNPP, ta zargi Gwamnan jihar Kano da shirya magudin zabe
  • Umar Doguwa ya ce Abdullahi Umar Ganduje ya yi shirin amfani da ‘yan daba a zaben yau
  • Shugaban NNPP ya ce burin Gwamnati shi ne a tada rigima, sai a kakaba dokar hana fita

Kano - Shugaban NNPP na reshen jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ya fitar da jawabi jiya, yana cewa ana niyyar haddasa tashin-tashina.

Daily Nigerian ta rahoto Doguwa yana cewa Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya yi wani zaman sirri da jami’an tsaro a kan wannan manufa.

Bayan zargin shugaban na NNPP, ba mu ji martani daga bangaren gwamnati ba, sai dai Doguwa bai iya bada wata hujja da za ta gaskata shi ba.

Kano - Shugaban NNPP na reshen jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ya fitar da jawabi yana mai cewa ana niyyar haddasa tashin-tashina.

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

Dabarar da ake shirin yi - Doguwa

Jam’iyyar NNPP ta ce Gwamnatin Ganduje ta na so ta haramta zirga-zirgan motoci da yadda mutane za su ganagara zuwa wuraren da za su yi zabensu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hon. Doguwa ya ce Mai girma Gwamna ya yi hayar ‘yan daba da za su tarwatsa rumfunan zabe a akalla kananan hukumomi 14 da ake da su.

'Yan sanda a Kano
Motocin 'Yan sanda a Kano Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Facebook

Tsakanin 2:30 zuwa 4:00, jam’iyyar adawar ta ce za a nemi a birkita ko ina, har da kasuwanni da ofishin INEC, don haka sai a sa dokar hana fita.

Daga nan ne sai a watse a bar jami’an INEC a ofishin tattara zabe, sai a samu hanyar murdiya.

Shirin da 'Yan Sanda suka yi

A gefe guda, an ji Shugaban ‘yan sanda, Usman Alkali Baba ya yi tanadin motoci da kayan aiki na musamman domin hana magudin zabe a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Ta Janye Zanga-Zangar Lumana Kan DSS A Kano

Leadership ta ce IGP ya aiko da jirgi daga sashen harkokin sama na rundunar ‘yan sanda da kuma motoci da karin makamai da kayan aiki domin zabe.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da jawabi, yana mai cewa sun karbi wadannan kaya domin yakar magudi.

Sabon kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel ya karbi wadannan kaya a jiya.

A jawabinsa, an fahimci cewa jami’an ‘yan sanda sun gama duk wani shiri na ganin an yi zabe lafiya, tare da jan kunnen duk masu niyyar tada rikici.

Zaben Kano a yau

Ku na da labari kusan jam’iyyu bakwai ne suke neman mulkin Kano, an tsaida Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf, Sadiq Wali a APC, NNPP da PDP.

Sauran ‘yan takaran su ne Sha’aban Sharada, Ibrahim Khalil, Salihu Tanko Yakassai da Bala Gwagwarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel