Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana Yau a Jihohin Kano Da Jigawa
Rana bata karya!
Allah ya kawo mu ranar zaben gwamnoni a Najeriya inda zamu kawo muku abinda ke gudana daga jihohin Kano da Jigawa.
A Kano, Abba Kabir Yusuf na NNPP zai fafata da Nasiru Yusuf Gawuna na APC, Aminu Wali na PDP, Sha'aban Sharada na ADP, Salihu Tanko Yakassai na PRP.
A Jigawa kuwa, Mataimakin Gwamna Namadi na son zarcewa kan kujerarsa maigidansa yayinda Mustapha Sule Lamido na PDP na kokarin bin sahun mahaifinsa.
Yan daba sun kai hari a Kano sun sace akwatin zabe
Wasu yan daba sun kai hari rumfar zabe da ke Chiranci a karamar hukumar Gwale ta Kano.
Sun sace akwatin zabe sun kuma kai wa masu zabe hari.
Yan sanda sun iso sun fatattake su, sun kwato akwatin zaben.
An kuma kama guda daya daga cikinsu.
Mustapha Sule Lamido, dan takarar gwamna na PDP a Jigawa ya isa rumfar zabensa
Mustapha Sule Lamido, dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic, Party, PDP a Kano ya isa rumfar zabensa don kada kuri'a.

Asali: Twitter
Salihu Tanko Yakasai, dan takarar gwamnan PRP a Kano ya yi zabe
Salihu Tanko Yakasai (Dawisu), dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PRP da matarsa sun kada kuri'arsu.
Tsohon hadimin na Gwamna Ganduje ya ce ana zabe lami-lafiya a yankinsa kuma ya shawarci mutane su fita su kada kuri'arsu.
Ya kuma kara da cewa an samu cigaba a bangaren INEC fiye da yadda ta kasance yayin zaben shugaban kasa na baya-bayan nan.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Yan daba sun lalata kayan zabe a Mazugal, karamar hukumar Dala, Kano
Yan daba sun lalata kayayyakin zabe filin Safari, gundumar Mazugal, karamar hukumar Dala ta Jihar Kano.
Wasu daga cikin wadanda suka fito zabe sun ce sun san wadanda suka lalata kayan kamar yadda suke fadi a cikin bidiyon.
Gawuna ya yi zabe a Kano, ya nuna takardar kada zabensa
Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamna na Jihar Kano ya kada kuri'arsa kuma ya daga kuri'arsa ya nuna, tamkar dai yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yayin zaben shugaban kasa da aka yi a baya-bayan nan.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
An kama jami'in NSCDC na bogi a Kano
Jami'an yan sanda sun kama jami'in hukumar tsaro ta NSCDC na bogi. An tisa keyarsa an saka shi cikin motar yan sanda.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Hotuna daga wani akwatin zabe a karamar hukumar Kano Municipal, Jihar Kano
Al'umma sun fara taruwa sannan ma'aikatan zabe na shiri domin fara tatance masu kada kuri'a
Ana shirye-shiryen fara zabe a wani rumfar zabe da ke karamar hukumar Kano Municipal a yau Asabar 18 ga watan Maris.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
An fara kada kuri'a a wasu akwatunan zabe a Kano
An fara kada kuri'a a akwatin zabe mai lamba PU 041, Gawuna Ward, Karamar hukumar Nassarawa ta Kano.
An fara misalin karfe 9 na safe.

Asali: Twitter
Bidiyon rikicin da ya barke tsakanin wakilan jam'iyyar APC da NNPP a rumfar zabe.
An samu rashin jituwa tsakanin wakilan jam'iyyun APC da NNPP a akwatin zabe mai lamba 004, Arzai, Karamar Hukumar Dala ta Jihar Kano.
Bidiyon na kasa: