'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP
- Muhammad Sani Abdullahi bai gamsu da sakamakon zaben ‘yan majalisar tarayya da aka yi ba
- ‘Dan takaran Sanatan na jam’iyyar APC ya ce hujjoji sun nuna masu an yi magudi a Kaduna ta tsakiya
- Dattijo yana ikirarin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun ba PDP gudumuwa wajen shan kashinsu
Kaduna - Muhammad Sani Abdullahi wanda ya nemi zama Sanatan Kaduna ta Tskiya a jam’iyyar APC, ya nuna cewa zai shigar da karar zaben 2023.
Malam Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo ya yi magana a Facebook yana cewa ya ga alamun an yi murdiya a zaben da ya wuce.
Tsohon Kwamishinan kasafin na jihar Kaduna ya ce sun gano an yi magudi, coge, sabawa dokar zabe, baya ga kin amfani da na’urar BVAS wajen yin zabe.
A zaben ‘dan majalisar dattawa na shiyyar tsakiyar Kaduna, Dattijo ya ce akwai rumfunan da aka yi aiki da takardun da INEC ba ta san da zamansu ba.
Shafin INEC ya tona asiri
‘Dan siyasar yake cewa sun samu wadannan hujjoji ne daga bayanan da ke shafin INEC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabin da ya yi ranar Alhamis a shafinsa, Abdullahi ya ce akwai kananan hukumomin da aka sanar da zaben da ya bambanta da sakamakon mazabu.
Ganin haka, Sani Abdullahi wanda ya yi aiki a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin Kaduna ya ce lallai za su shigar da kara a kotun zabe.
‘Dan takaran na APC yake cewa su na sa ran idan aka yi gaskiya a shari’a, za a ba jam’iyyarsa nasara. PDP ce ta lashe duka kujerar Sanatocin jihar Kaduna.
'Yan APC sun yi zagon-kasa
‘Dan takaran Sanatan ya ce sun gano ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun bada gudumuwa a wajen nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a zaben na bana.
A dalilin haka aka tattara hujjoji domin gabatarwa uwar jam’iyya, a hakunta wadanda suka yi wa APC makarkashiya kamar yadda doka ta yi tanadi.
Mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ta hada da Birnin Gwari, Kaduna ta Arewa, Igabi, Giwa, Kaduna ta Kudu, Chikun da kuma Kajuru.

Ya aka yi Atiku ya ci Osun?
An ji labari Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso yamma ya fallasa Sakataren jam’iyya na kasa da zargin ya cinye kudin kamfe a jiharsa.
Dr. Salihu Lukman ya ce Sanata Iyiola Omisore jawo Atiku Abubakar ya doke Bola Tinubu a Osun.
Asali: Legit.ng