Jam'iyyar SDP Ta Bayyana Gaskiya Kan Dakatar Da Dan Takarar Gwamnan Ta a Nasarawa

Jam'iyyar SDP Ta Bayyana Gaskiya Kan Dakatar Da Dan Takarar Gwamnan Ta a Nasarawa

  • Jam'iyyar Social Democratic Party ta musanta ƙarerayin dake yawo cewa ta dakatar da ɗan takarar gwamnan ta na jihar Nasarawa
  • Jam'iyyar ta bayyan cewa waɗannan labaran dake yawo ba komai bane face labarai ne waɗanda basu da tushe ballantana makama
  • Jam'iyyar ta kuma nuna goyon bayan ta ga ɗan takarar gwamnan ta na jihar da dukkanin ƴan takarar ta a zaɓen ranar Asabar

Jihar Nasarawa- Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), ta bayyana cewa bata dakatar da ɗan takarar gwamnan ta na jihar Nasarawa ba, Hon Mohammed Alfa Mustapha, inda ta ƙara da cewa har yanzu shine sahihin ɗan takararta.

A cewar jam'iyyar mutane su yi watsi da labaran kanzon kuregen da ake yaɗawa cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar na jihar Nasarawa ya dakatar da ɗan takarar gwamnan. Rahoton Leadership

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe Dan Takarar Gwamna Yasha Da Kyar a Wani Mummunan Harin Da Aka Kai Masa

Jam'iyyar SDP
Jam'iyyar SDP Ta Bayyana Gaskiya Kan Dakatar Da Dan Takarar Gwamnan Ta a Nasarawa Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

A wata sanarwa da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Dr Olu Ogunloye, ya fitar, ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar na jiha ko kwamitin gudanrwar ba su da hurumin dakatar da ɗan takarar ko hana shi yin takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar SDP.

Sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ƙarya ce tsagwaronta shugaban jam'iyyar na jiha ko wani yace an bashi umurni daga sama yayi ƙoƙarin dakatarwa ko korar ɗan takarar gwamnan mu, Hon Mohammed Alfa Mustapha, daga jam'iyyar ana dab da zaɓe."
Babu ko ɗaya daga shugaban jam'iyya na ƙasa da kwamitin gudanarwa na ƙasa da ya amincewa shugaban jam'iyyar na jiha ya dakatar da ɗan takarar gwamnan."
"Uwar jam'iyya ta ƙasa ta warware wannan ƙulle-ƙullen da shugaban jam'iyyar na jiha yake yi.
“Ina faɗi da babbar murya cewa gabaɗaya uwar jam'iyyar SDP tana tare da Hon Mohammed Alfa Mustapha da dukkanin ƴan takarar jam'iyyar SDP a jihar Nasarawa."

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Shugaban Jam’iyyar PDP Na Jihar Ebonyi Ya Goyi Bayan Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC

A wani labarin na daban kuma, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ebonyi ya juyawa jam'iyyar sa baya ana dab da zaɓe.

Shugaban jam'iyyar ya nuna goyon bayan sa ga ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel