Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Gwamnan APC, Suna Nemansa Suna Cewa 'Lokacin Mutuwarsa Ta Yi'

Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Gwamnan APC, Suna Nemansa Suna Cewa 'Lokacin Mutuwarsa Ta Yi'

  • Yan bindiga sun kai hari gidan iyalan dan takarar gwamnan Oya na jam'iyyar APC, Teslim Folarin da nufin hallaka shi
  • Shaidun gani da ido sun ce da yawa daga cikinsu sun ji raunuka yayin da su ke gudun tsira da rayuwarsu lokacin da yan bindigar ke harbi kan mai uwa da wabi
  • Mai magana da yawun dan takarar ya ce sun mika koken su ga jami'an tsaro don a gano tare da hukunta wanda su ka dauki nauyi da wanda su ka aikata harin

Ibadan, Oyo - Mutane da dama sun jikkata lokacin da ake zargin yan bindiga sun mamaye gidan iyalan dan takarar gwamnan Jihar Oyo a tutar jam'iyyar APC, Sanata Teslim Folarin, rahoton The Nation.

Shaidun gani da ido sun ce yan bindigar sun mamaye Oja'gbo a karamar hukumar Kudu maso gashin Ibadan a motoci 10 kirar Toyota Hilux da rufaffun lambobin mota da misalin 8:00 na daren Alhamis.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Mutum 4 Yayin Arangama Tsakanin Yan Shi'a Da Tawagar El-Rufai A Kaduna

Folarin
Yan Bindiga Sun Tafi Gidan Dan Takarar Gwamnan APC Don Su Sheke Shi. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Shaidu sun magantu kan afkuwar harin

Shaidun gani da idon sun ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

''Mun tsallake mutiwa da kyar a hannun maharan amma da yawa daga cikinmu sun ji raunika daban daban yayin da mu ke gudun tsira.
''Yan bindigar na sanye da bakaken kanya sun kuma rufe fuska da farar hular rufe fuska. Su na ihun 'ina Folarin, iku lokan E (lokacin mutuwarka ya yi) yayin da su ke harbi akan iska. Sun balle fadar Oja'gbo su na neman Oloye.
''Sun tarwatsa daruruwan mu da ke jiran Sanata Folarin da harbi. Allah ya kwaci rayuwarmu.''

Hadimin Folarin ya tabbatar da harin

Mai taimaka Folarin akan kafafen yada labarai, Yekini Olaniyi ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa da safiyar Juma'a.

Ya ce:

''Misalin 8:10 na daren Alhamis, 16 ga watan Maris, wasu gungun yan bindiga kimanin 30 cikin motoci 10, su ka mamaye gidan iyalan Sanata Teslim Folarin da yunkurin hallaka rayuwarshi.''

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

''Sun yi zaton Oloye Folarin ya na nan lokacin da su ke kokarin aiwatar da kisan. Sanata Folarin ya shirya ganawa da yan majalisar sarki a fadar Oja'gbo daren jiya amma bai samu hallata ba saboda wani zaman tattaunawa da ma su ruwa da tsaki na Jihar Oyo a gidan yada labarai na YES FM.''
''Kun san Oloye Folarin shi ne Mogajin gidan zuri'arsa, Ile Baale a Oja'gbo da ke Ibadan kuma Asaaju Olubadan na kasar Ibadan. Ya shirya ganawa da iyalansa a fadarsa amma ba a samu hakan ba. Yan bindigar da ba a san ko su waye ba sun yi tunanin ya shiga tattaunawar lokacin da su ke yunkurin hallaka shi amma Allah ya ceci rayuwarsa.''
''Mun sanar da jami'an tsaro don su binciki lamarin, da su gano wanda su ka aikata laifin da wanda su ka dauki nauyinsu don daukar mataki.''

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan Oyo, Adewale Osifeso ya yi alkawarin zai yi bayani daga baya.

Kara karanta wannan

Dakarun MNJTF Sun Cafke Iyalai Da Masu Taimakawa Boko Haram 900 a Dajin Sambisa

Bai yi bayani ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton.

Kusa a jam'iyyar PDP ya yi murabus yan awanni kafin zaben gwamna

A baya, kun ji cewa jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta, Dele Omenogor ya fita daga jam'iyyar ana yan awanni zaben gwamna na ranar Asabar.

Omenogor ya koka da cewa gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa ta yi watsi da masarautar Amai da daukakin kasar Ukwuani, hakan yasa ya fice daga PDPn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel