Allura Na Kokarin Tona Garma a Zargin Cinye N500m Na Kamfe a Jam’iyyar APC
- A maimakon rigimar Salihu Lukman da Iyiola Omisore ta lafa, abubuwa su na kara jagwalgwalewa
- An ji Dr. Iyiola Omisore ya fitar da wani jawabi a matsayin raddi ga Sakataren Jam’iyyar APC na kasa
- Mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma ya taso Sakatarensa a gaba dalilin fadi zabe a Osun
Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso yamma, Salihu Lukman yana nan a kan batun na zargin da yake yi wa Iyiola Omisore.
The Guardian ta rahoto cewa Dr. Salihu Lukman ya sake yin kira ga Sakataren APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore ya fito da kudin kamfe a jihar Osun.
Dr. Lukman yana maida martani ga barazanar da aka ji Iyiola Omisore yana yi masa, yana cewa zai kai shi kotu a kan zargin bata masa suna da kima.
‘Dan siyasar ya ce daukar hayar Lauya da sakataren APC na kasa ya yi ba zai tsorata shi ba a wajen ganin ya bukaci ayi abin da ya kamata a jam’iyya.
Lukman ya fitar da martani
Lukman ya fitar da jawabi ‘Re: APC Internal Dynamics and Future of Democracy’. watau raddin abubuwan da ke faruwa da makomar damukaradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban APC mai mulki yana ganin babu wanda ya jawo jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar suka doke Bola Tinubu a Osun a zaben bana illa Omisore.
Adamu da Iyiola Omisore su bar NWC
A nan ne Lukman ya kara yin kira ga Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore wanda shi ne Sakatare da su yi murabus daga kujerunsu.
The Cable ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa wannan shi ne abin da shugabannin na jam’iyyarsu ta APC za su yi domin zababbun ‘yan majalisa su girmama su.
“Ina yin wannan kira cikin girmamawa ba tare da rike kowa a rai ba, har da Iyiola Omisore.
Ina kan magana ta cewa Omisore ya gagara hada-kan shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyyar a jihar Osun wanda hakan ne sanadiyyar shan kashinmu a zaben.
Yana adawa ga kokarin ganin an yi gaskiya, ya koma yin barazana. Menene damukaradiyya idan babu ke-ke-da-ke-ke, dole ne Omisore ya fito da gaskiya.”
- Dr. Salihu Lukman
Bukatar Concern Christians of Nigeria
Tun da Bola Tinubu da Kashim Shettima Musulmai ne, rahoto ya zo cewa Kiristoci su na so a ba su mukamai masu tsoka a gwamnatin da za a kafa a Mayu.
Wata kungiyar Kiristoci ta 'Concern Christians of Nigeria' ta na neman Sakataren Gwamnati da kujerar shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng