Tinubu: "Ban San Batun Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Aso Rock ba" - Gbajabiamila

Tinubu: "Ban San Batun Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Aso Rock ba" - Gbajabiamila

  • A farkon makon nan Abdullahi Adamu, Kashim Shettima su ka zauna da zababbun ‘Yan Majalisa
  • Femi Gbajabiamila ya karyata jita-jitar cewa ya hakura da kujerar majalisar wakilan tarayyarsa
  • Shugaban majalisar ya ce batun cewa yana jiran Bola Tinubu ya ba shi kujerar COS, ba gaskiya ba ne

Abuja - Femi Gabjabiamila wanda yake rike da kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya ya musanya jita-jitar neman mukami da ake yi masa.

Ana yada cewa Rt. Hon. Femi Gabjabiamila ya na so ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, The Cable ta ce ‘dan siyasar ya karyata haka.

Shugaban majalisar ya musanya rade-radin ne bayan zaman da zababbun ‘yan majalisa suka yi da Bola Tinubu a fadar Aso Rock a ranar Litinin.

Duk surutan da ake yadawa, Femi Gabjabiamila ya nuna bai san komai kan neman mukami ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

“Ban san komai a game da batun neman zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ba.
Abin da kurum na ji shi ne ban zo karbar satifiket dina a makon jiya ba saboda wannan dalili, wani ya yi tunanin haka, saboda yana ganin ban damu da kujera ta ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Femi Gbajabiamila

Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila a Aso Rock Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

Meya hana Gabjabiamila karbar satifiket?

Jaridar nan ta Leadership ta rahoto ‘dan majalisar wakilan tarayyar na mazabar Surulere ya ce kamfe da suke yi wa APC a Legas ya hana sa zuwa Abuja.

Bayan zaben 2019, ‘dan siyasar ya nuna bai karbi satifiket da wuri a hannun hukumar INEC, a wannan karo ma uzurin kamfe ya hana shi zuwa sai daga baya.

"Ina Legas, ba zan iya barin gari ba saboda ina yi wa jam’iyya ta kamfe. Abu na farko kenan.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Sannan zai ba ku sha’awa ku sani cewa shekaru hudu da suka wuce, ban zo nan karbar takardar shaidar lashe zabe ba saboda ban samu halarta ba.
Ba na tunanin wannan wani abin magana ne, yau ko gobe zan karbi takardar shaidar cin zabe na."

- Femi Gbajabiamila

Tinubu bai da 'dan takara a Majalisa

Bola Tinubu ya fadawa zababbun ‘yan majalisar tarayya matsayarsa a kan rabon mukamai. An ji Tinubu ya yi jawabi ne da yawun Kashim Shettima.

Maganar wadanda za su zama shugabanni a majalisar tarayya bai gaban Tinubu. Shugaban kasan na gobe ya karkata wajen zaben Gwamna a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng