Yadda Tambuwal da Shugabannin PDP Suka Haddasa Shan Kashin Atiku – Jigon PDP
- Murtala Adamu Kimba ya ce na-kusa da Atiku Abubakar suka kai Jam’iyyar PDP suka baro ta
- ‘Dan siyasar yake cewa Aminu Tambuwal suka yi sanadiyyar tashin Rabiu Kwankwaso daga PDP
- A ra’ayin Kimba, shugabannin jam’iyyar PDP na kasa ba su yi kokari wajen dinke barakar G5
Abuja - Murtala Adamu Kimba wanda yana cikin kusoshi a jam’iyyar PDP, yana ganin rikicin gida ya jawowa Atiku Abubakar fadi zaben bana.
Da yake yi wa manema labarai bayani a garin Abuja, Murtala Adamu Kimba ya ce an yi watsi da wasu masu ruwa da tsaki saboda manyan jam’iyya.
Daily Trust ta rahoto ‘dan siyasar yana mai cewa tun da Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi suka sauya-sheka, aka hango rashin nasarar PDP.
Bayan Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun bar jam’iyyar PDP, sai Gwamnonin kungiyar G5 suka fara botsarewa shugabancin Iyorchia Ayu.
Silar rikicin gidan PDP
"Lokacin da aka ware kujerar Mataimakin shugaban jam’iyya zuwa Kano, Katsina da Jigawa, sai Gwamna Aminu Tambuwal yake so ya tura mutuminsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalili kuwa saboda Gwamnan Sokoto yana burin samun takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Kwankwaso ya tafi NNPP
Wannan batun shugabanci ya jawo rikici, sai tsohon Gwamnan na kano ya tafi. A zaben tsaida gwani sai (Tambuwal) ya janyewa Atiku da ya yi nasara.
Hakan ya jawo wasu har da Gwamna Wike ba su ji dadin abin da ya faru, wannan ne ya yi sanadiyyar kafa kungiyar G5 ta Gwamnonin jihohi.
Gwamna Wike ya rike PDP tun 2015, har bayan zaben tsaida gwani ya yi tunanin zai samu takarar mataimakin shugaban kasa, amma bai yi nasara ba.
Bayan zaben tsaida gwani, jam’iyyar ta gagara sasanta rikicin gidanta lokacin da G5 suka ce bai dace a rike shugabancin jam’iyya da takara ba.
- Murtala Adamu Kimba
An rahoto ‘dan siyasar yana mai cewa na-kusa da Atiku Abubakar suka hura wutan rikicin, a karshe ba su iya doke APC a jihohin da suka fito.
Asali: Legit.ng