Shin Kwankwaso Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Murna, NNPP Ta Yi Karin Haske
- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ragargaji zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, ta kira shi zababben da INEC ta tursasa
- Agbo Major, mai magana da yawun jam'iyyar, ya furta hakan yayin da ya ke karyata rahoton da ke cewa dan takarar shugaban kasarsu Rabiu Kwankwaso ya taya Tinubu murna
- Major ya ce dan takarar shugaban kasar jam'iyyarsu ba zai iya taya Tinubu murna ba kan nasararsa mai alamar tambaya da wasu yan takarar ke ikirarin suma sun ci zaben
FCT, Abuja - Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasarta, Rabiu Kwankwaso ya taya zababen shugaban kasa, Bola Tinubu, murna.
Kakakin NNPP, Agbo Major ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Maris, The Punch ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Major ya ce:
"Rahoton cewa Injiniya Kwankwaso ya taya Tinubu murna mafarki ne na wasu masu marasa son dimokradiyya, yan kwangilar siyasa da kuma masu yada karya da ke son amfani da farin jinin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar."
NNPP ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 - Major
Major ya dage cewa zaben shugaban kasa na 2023 da aka kammala na cike da kurakurai kuma ba abin amincewa bane.
Kakakin na NNPP ya ce:
"NNPP ba ta amince da sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu ba domin bai dace da ra'ayin yan Najeriya ba da suka fito kwansu da kwarkwata suka yi zabe amma INEC ta basu kunya don gaza yin zabe mai nagarta da rashin cika alkawarin tura sakamakon zabe kai tsaye zuwa intanet daga akwatin zabe wanda da hakan ya tabbatar da sahihancin wanda ya ci zaben shugaban kasar.
"Abin bakin ciki, zaben shugaban kasar ya zama wasa ne kawai don yan Najeriya da masu sa ido na kasashen waje ba su gamsu ba. Yan fashin siyasa wadanda ba su son a samu sabuwar Najeriya idan an zabi jam'iyyar mu suka aikata wannan abin."
Wanda ya lashe zabe da INEC ta tursasa: NNPP ta soki Tinubu
Kakakin na NNPP ya ce dan takarar jam'iyyarsa ba zai iya taya Tinubu murna ba kan nasararsa mai alamar tambaya da sauran yan takara suka cewa sune suka yi nasara kuma sun tafi kotu.
Ya ce:
"Dukkan masu don dimokradiyya, tsarin doka za su jira kotu ta yanke hukunci.
"Har sai kotu ta yi hukunci, ba zai dace NNPP da aka yi wa magudi a sassan kasa ba ta amshi kaye ta taya wanda INEC suka tursasa mana murna."
Ayodele Fayose: Ina nan a PDP, ban fita ba
Ayo Fayose, Jigon PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya karyata rahoton cewa ya fita daga jam'iyyar PDP.
Fayose ya yi karin bayani yana mai cewa yana nan daram a PDP amma ya dan koma gefe ne don ya samu ikon yin wasu maganganu a matsayinsa na dan kasa.
Asali: Legit.ng