Ranar Mata ta Duniya: Mata 2 da Suka Shiga Jerin ‘Yan siyasa 109 da Za su Zama Sanatocin Najeriya a 2023

Ranar Mata ta Duniya: Mata 2 da Suka Shiga Jerin ‘Yan siyasa 109 da Za su Zama Sanatocin Najeriya a 2023

  • ‘Yan siyasa kimanin 100 Hukumar INEC ta ba takardar shaidar lashe zaben Majalisar Dattawa
  • A 2023 za a sake samun karancin mata a majalisar dattawa, maza sun karbe kusan duka kujerun
  • Bayan Ireti Kingibe da Banigo I. Harry, babu wata mace a cikin ‘yan takaran Sanata da tayi nasara

Abuja - Hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar da sunayen wadanda suka lashe zaben Sanatoci da aka yi a ranar 25 ga watan Fubrairun 2023.

A ranar 1 ga watan Yuni, nan da kwanaki kusan 83 za a rantsar da zababbun ‘yan majalisar a matsayin Sanatocin da za su wakilci mazabunsu.

Legit.ng Hausa ta fahimci a cikin wadanda za a rantsar nan da watanni uku, mata biyu kurum ake da su, ma’ana kasonsu bai kai 2% a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Abin Sani Game Da ‘Yan Takara 6 da ke Hangen Kujerar El-Rufai a Kaduna

A tarihin Najeriya an samu mata kamar Nenedi Esther Usman, Aisha Jummai Alhassan, Binta M. Garba, Aisha Binani da suka zama Sanatoci.

Su wanene wadannan mata?

Matan da suka yi nasara a wajen neman takarar Sanata sun hada da Ireti Heebah Kingibe wanda za ta wakilci mutanen Abuja a inuwar LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ireti Heebah Kingibe ta taba auren Babagana Kingibe wanda ya nemi Shugaban kasa a 1993, kuma ya rike Sakataren gwamnatin tarayya a 2007.

Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan a Majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Mace ta biyu da za ta zama Sanatan Najeriya a shekarar nan ita ce Banigo I. Harry wanda ta lashe zaben Sanatar Ribas ta yamma a karkashin PDP.

Ba a zaben nan Banigo Harry ta fara kafa tarihi ba, tun 2015 ta zama macen farko da aka rantsar a matsayin mataimakiyar Gwamna a jihar Ribas.

'Yar siyasar ta rike Darekta, Kwamishina, Darekta Janar da Sakataren din-din-din a ma'aikatar lafiyar Ribas kafin ta zama Sakatariyar gwamnati.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: INEC ta fito da kayan aikin zabe, ta fara raba su a wata jihar Arewa

Kujeru 7 suka rage

Har yau mutanen Enugu ta gabas ba su san wanda zai wakilce su a majalisa ba, hakan ya faru ne a sakamakon kashe ‘dan takaran Sanata na LP.

Sauran kujerun da ba a san wanda zai yi nasara ba sun hada da na Kebbi ta Arewa, Yobe ta Kudu da kuma duka Sanatoci uku da ke jihar Sokoto.

Har ila yau, hukumar INEC ba ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben Sanata Zamfara tsakiya ba, amma kusan da wahala mace ta ci kujerar.

Takarar 'ya 'yan manya

A zaben bana, an ji labari yaron Jerry Gana ya ci kujerar majalisa yadda Mai dakin Ministan harkoki na musamman ta yi nasara a jihar Benuwai.

'Ya 'yan Gwamnonin Kano da Kaduna su nemi takara a jam'iyyar APC, amma Bello El-Rufai ne kurum ya yi nasara, NNPP ta doke Abba Ganduje.

Kara karanta wannan

Matsala ta faru: Jerin mazabun sanata 8 da dole za a sake zabe, INEC ta fadi yaushe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng