An Fara Zawarcin Mukamai a Gwamnatin Zababben Shugaban Kasa Tinubu
- Kungiyoyi daban-daban a kasar sun fara zawarcin mukamai a sabuwar gwamnati da ake shirin kafawa a watan Mayu
- Kungiyar mata Musulmai na kasa sun bukaci zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya baiwa mata kaso 50 na mukamai a gwamnatinsa
- Yan asalin Abuja sun mika kokon bararsu a gaban Tinubu cewa ya ba daya daga cikinsu ministan babban birnin tarayya
Bayan hukumar zabe ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa a babban zaben 2023, kungiyoyi sun fara kamun kafa domin samun mukamai a gwamnati mai zuwa.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne za a rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu.
Kungiyar mata Musulmai na Najeriya wato FOMWAN ta bukaci zababben shugaban kasa Tinubu da ya ba matan Najeriya kaso 50 na mukaman siyasa.
Kungiyar ta taya Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima murnar nasarar lashe zaben shugaban kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar FOMWAN na kasa, Hajia Rafiah Sanni, ta gabatar da sakon ga Tinubu a wata sanarwa a Ilorin, jihar Kwara, rahoton Leadership.
Kungiyar Musuluncin ta jinjinawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kan gudanar da zabe na gaskiya da amana.
Ta bukaci fusatattun jam'iyyu da yan takararsu da su nemi hakkinsu a kotu sannan su guji duk kalaman tunzurawa da ka iya kawo hargitsi a kasar.
Sai dai kuma, kungiyar ta yi korafin cewa tsarin siyasar Najeriya baya yi wa mata adalci, tana mai cewa:
"Hakan ya tabbata da adadin kujerun da mata suka samu a majalisar dokokin tarayya da nade-naden da aka yi a majalisun."
"FOMWAN ta yarda cewa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) har jam'iyyun adawa babu wanda zai iya cin zabe a rumfar zabe ba tare da kuri'u masu yawa daga mata ba.
"Don haka muna rokon zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima da su kawo sauyi ta hanyar tabbatar da cewa kwararrun mata a fadin al'adu da addinai sun samu mukaman da suka dace. Muna neman a ba mata kaso 50 na nade-nade."
Ka bamu ministan Abuja, asalin yan birnin tarayya ga zababben shugaban kasa
A nasu bangaren, asalin yan babban birnin tarayya sun roki zababben shugaban kasa Tinubu da ya ba dan asalin Abuja mukamin minista idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Mazauna birnin tarayyan karkashin kungiyar GICC reshen Birnin tarayya sun kuma roki a aiwatar da tsarin siyasa da gwamnati kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin 1999, don kawar da duk wani wariyar da ake nunawa yan asalin Abuja.
Shugabannin arewa maso gabas sun nemi a fadada gwamnati
Har ila yau, shugabannin kiungiyar raya arewa maso gabas wato NEDA, sun yi kira ga Tinubu da ya gudanar da gwamnati da za ta dama da kowa sannan ya kalli Najeriya a matsayin tsintiya madaurinki daya.
Sun kuma bukaci zababben shugaban kasar da ya yi shugabanci ba tare da la'akari da kabila, addini da banbancin siyasa ba da zaran an rantsar da shi a watan Mayu, rahoton Leadership.
A wani taron manema labarai a Bauchi, babban sakataren kungiyar, kwamrad Bitako Abubakar Umar, ya taya zababben shugaban kasar, Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima murna.
Umar ya bayyana nasararsu a matsayin wata alama da ke nuna cewa Najeriya da yan Najeriya sun fara barin siyasar addini da na kabilanci.
Ya kuma bayyana cewa an yi zabe sannan an ayyana wanda ya ci zabe don haka duk wanda bai gamsu ba, akwai tanadi na neman gyara karkashin kundin tsarin mulki wanda dukkanin yan kasa suka yi rantsuwar riko da shi.
Allah ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so
A wani labarin, sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad III, ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya da su zamo masu biyayya ga shugabanninsu don Allah ne kai bayar da mulki ga wanda ya so.
Asali: Legit.ng